Harkar ilmi: Kwankwaso ya ziyarci Indiya saboda a tura Yara Digirgir
Mun samu labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya bar Najeriya zuwa kasar waje domin fara shirye-shiryen tura wasu Matasan jihar Kano zuwa karatu.
Kamar yadda mu ka samu labari daga bakin wani na-kusa da tsohon gwamnan na jihar Kano mai suna Saifullahi Mohammed, yanzu haka Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara zuwa Indiya a kan wannan batun.
Kwankwaso ya gana da shugabannin jami’ar nan ta Shardah da kuma Mewar da ke cikin kasar Indiya inda a ke sa rai za a tura wasu daga cikin Hazikan Matasan Kano su fara karatu a wannan zango na 2019.
A na sa rai za a samu wasu daga cikin mutum 370 da wannan gidauniya ta zakulo da za su yi karatunsu na Digirgir watau Masters a wadannan jami’o’i da ke cikin Garin Delhi da kuma Chittorgarh.
KU KARANTA: Gidauniyar Kwankwasiyya ta tara miliyoyi domin tura Talakawa karatu
Idan ba ku manta ba, Gidauniyar Kwankwasiyya ta zabi wasu zarata da su ka kammala jami’a da matakin Digiri na farko, inda a ka sha alwashin turasu karatu zuwa kasashen ketare domin su kara karatu.
A lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso ya na gwamna a jihar Kano, ya tura Matasan jihar masu kasa da shekara 30 fiye da 2600 domin su yi karatun Digiri a jami’o’i da dama da ke kasashen waje.
Rabiu Kwankwaso ya na ganin cewa ilmantar da wadannan Matasa shi ne zai habaka jihar ya rage rashin aikinyi tare da kawo saukin barna da a ke aikatawa don haka su ka shirya gidauniya domin wannan.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng