Ugwuanyi ya zabi Okocha mai bada shawara wajen gyara harkar wasanni

Ugwuanyi ya zabi Okocha mai bada shawara wajen gyara harkar wasanni

Tsohon ‘Dan wasan kwallon kafan Najeriya, Austin ‘Jay Jay’ Okocha, wanda ya taba rikewa Super Eagles kambu ya na cikin wadanda a ka ba wasu mukamai na musamman a jihar Enugu.

Kamar yadda mu ka samu labari jiya daga Jaridar Premium Times, gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu ya nada Jay Jay’ Okocha a cikin wanda za su yi bangarorin gwamnati garambawul.

Mai girma Ugwuanyi ya kaddamar da tsohon ‘dan wasan kasar da kuma wasu kwararru a kowane fanni da a ka zabo a fadin jihar domin su rika ba gwamnatin Enugu shawarar hanyoyin gyara.

Daga cikin wadanda a ka zaba su yi wannan aiki akwai tsohon Darekta Janar na hukumar NBC na kasa, Mista Emeka Mbah. Wadannan su ne sahun karshe da gwamnatin Enugu ta ba wannan aiki.

KU KARANTA: Saboda tsohon Kocin Najeriya na ke so mu ci Kofi - 'Dan wasa

Okocha shi ne Mai bada shawara na musamman a wannan bangare a kan abin da ya shafi harkar Matasa da kuma wasanni, yayin da shi kuma Emeka Mbah zai zama shugaban wannan kwamiti.

Kafin nan gwamna Uguwanyi ya nada wanda za su taimaka masa wajen habaka bangaren ilmi, kiwon lafiya, aikin gwamnati, tsaro, shari’a da samar da ruwa da kuma kula da masarautun da ke jihar.

Tsohon kyaftin JJ Okocha ya buga kwallo a kasashe da dama da su ka hada da Faransa da Ingila a lokacin ya na ganiyar tashensa. Wannan ya sa gwamnatin jihar Enugu ta nemi aiki da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng