'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Kano, sun kubutar da yarinya mai shekara hudu

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Kano, sun kubutar da yarinya mai shekara hudu

Wata tawagar 'yan sanda na musamman daga jihar Kano sun kubutar da wata yarinya mai shekaru hudu, Khadijat Rilwanu, da masu garkuwa da mutane suka tafi da ita Kaduna bayan sun sace ta a Kano.

Wasu masu garkuwa da mutane su uku ne suka sace yarinyar a unguwar Naibawa da ke cikin garin Kano.

Da ya ke bajakolin masu laifin a hedikwatar 'yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai, kwamishinan 'yan sanda a jihar, Ahmed Iliyasu, ya ce an sace yarinyar nan a kusa da gidan iyayenta.

Ya kara da cewa wata tawagar jami'an 'yan sanda ce ta bi sahun masu garkuwa da yarinyar zuwa jihar Kaduna, inda aka same ta a gidan wata mata da ke aiki tare da masu garkuwa da mutanen. Ya kara da cewa an kubutar da yarinyar ne bayan ta shafe tsawon sati biyu tare da masu garkuwa da ita.

DUBA WANNAN: Harin kwanton bauna: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji 5, sun raunata da yawa

A cewar Iliyasu, "a ranar 4 ga watan Yuli ne wata tawagar jami'an 'yan sanda karkashin atisayen atisayen 'Puff Adder' ta samu nasarar kama wani mutum mai garkuwa da mutane mai suna Ibrahim Musa da ke zaune a Unguwar Rimi a Kaduna.

"Sanadiyyar binciken da aka gudanar a kansa ne aka gano wasu mata guda biyu da ke aiki tare da shi, wadanda kuma su ne ke ajiye da wata yarinya, Khadijat Rilwanu, mai shekaru hudu, da aka sato daga unguwar Wailari mai makwabtaka da Naibawa a cikin garin Kano."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel