Mamakon ruwan sama ya salwantar da rayuka 2, gidaje sun rushe a jihar Katsina da Kebbi

Mamakon ruwan sama ya salwantar da rayuka 2, gidaje sun rushe a jihar Katsina da Kebbi

Rayuwar wani saurayi Usman Jafaru, mai shekaru goma sha uku ta gamu da karshen ta tare da ta wani saurayin da manema labarai ba su samu masaniyar sunan sa ba.

Ajali dake zuwa babu shiri ballantana ankaraswa, ya katse hanzarin samarin biyu yayin saukar wani mamakon ruwan sama da sanyin safiya ta ranar Asabar 6, ga watan Yuli cikin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Mutane dama sun jikkata yayin saukar wannan ruwan sama tamkar da bakin kwarya kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, kimanin gidaje da makarantu 70 sun ruguje a sanadiyar saukar ruwan saman na mamako tare da iska mai karfin gaske musamman a garuruwan Sabuwar Unguwa, Gardirge, Sabon Garin-Malamai da kuma wasu yankuna daban-daban.

KARANTA KUMA: Gabanin karewar wa'adin gwamnatin Buhari za mu yi kidayar al'ummar Najeriya - NPC

Ruwan da ya sauka na tsawon sa'o'i uku ya janyo ambaliyar ruwa da tayi sanadiyar salwantar muhallan al'umma da dama.

Kazalika makamanciyar wannan annoba ta auku a jihar Kebbi inda ambaliyar ruwa tayi sanadiyar rushewar gidaje 40 da wata makarantar sakandire guda daya yayin da mutane kimanin 600 suka rasa muhallansu a karamar hukumar Dandi ta jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng