Rashin lafiya: An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya (Hotuna)

Rashin lafiya: An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya (Hotuna)

An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sani Idris, daya daga cikin kafafunsa sakamakon rashin lafiyar da ke damunsa.

Jarumi, Sani Idris, da aka fi sani da 'Moda' ya dade ya na kwance a asibiti, karkashin kulawar likitoci, bayan ciwon da ke damunsa ya yi tsanani.

Moda na fama da matsanancin ciwon sukari (Diabetes), kuma an kwatar da shi a asibiti tun cikin shekarar da ta gabata.

Halin da jarumin ke ciki ne suka jawo wassu kafafen yada labarai da ma'abota rubuta a dandalin sada zumunta suka fara jita-jitar cewa Moda ya mutu a cikin watan Mayu na shekarar 2018, kafin daga bisani ya fito ya bayya cewa yana nan da ransa.

Rashin lafiya: An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya (Hotuna)
An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya
Asali: Facebook

Rashin lafiya: An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya (Hotuna)
An yanke wa Moda kafa daya
Asali: Facebook

Tun bayan kwantar da Moda, manyan jaruman fina-finan Hausa da suka hada da Ali Nuhu da manyan darektoci irinsu Falalu Dorayi ke zarya zuwa asibitin da aka kwantar da shi domin duba lafiyarsa.

DUBA WANNAN: Tsoron Allah: Matashi 'mai shara' ya mayar da gwal na miliyan N249 da ya tsinta

Moda na daga cikin jaruman fina-finan Hausa da suka dade an dama wa da su a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood). Jarumin ya samo sunan 'Moda' ne sakamakon rawar da ya taka a wani tsohon shirin wasan Hausa mai suna 'Wasila'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel