Doguwa da Garo su na neman babbar kujerar APC a Majalisa
Har yanzu ba a kai ga karshen rikicin da a ke fama da shi a majalisa ba a dailin nade-naden manyan kujeru. Yanzu haka APC ta na fama da ciwon kai a kan wanda zai zama shugaban masu rinjaye.
APC ta zabi Honarabul Alhassan Ado Doguwa ne a matsayin shugaban masu rinjaye, amma wasu daga cikin ‘yan majalisa na APC sun fara nuna adawarsu a kan wannan zabi na uwar jam’iyya.
Wasu gungun ‘yan APC sun fi aminta ne da Honarabul Aminu Suleiman Goro a matsayin wanda zai rike wannan babbar kujera. Shi ma Honarabul Aminu Goro ya fito ne daga yankin na Kano.
A dalilin wannan, har yanzu majalisar ta gaza fitar da sunayen shugabanninta kamar yadda Daily Trust ta rahoto a Ranar 3 ga Watan Yuni, 2019. A na sa rai a cikin makon nan a karkare wannan.
KU KARANTA: Rigima ta barke a Majalisa bayan Kakaki ya nunawa PDP kunnen-kashi
Kawo yanzu Magoya bayan Aminu Sule Goro sun fara tattara sa-hannun wadanda ke tare da su a majalisar, haka zalika wadanda su ke tare da Alhassan Ado Doguwa su na kirga na su kuri’un.
Da zarar an kammala wannan kidaya, duk wanda ya fi yawan jama’a, shi ne zai samu wannan kujera kamar yadda mu ka fahimta bayan jam’iyya ta yi kokarin nuna fifiko a kan Ado Doguwa.
Aminu Suleiman Goro shi ne mai wakiltar Mazabar Fagge ta cikin birnin Kano a majalisar wakilan, yayin da Takwaransa Ado Doguwa ya ke wakiltar mutanen Tudunwada da Doguwa.
Hon. Aminu Goro ya dade a majalisa kamar Ado Doguwa. Sai dai Hon. Doguwa ya rike mukamin shugaban masu tsawatarwa a majalisa ta 9. A wannan karo, ‘yan majalisun na Kano za su gwabza.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng