Tirkashi murna za ta koma ciki: Kotu ta aikawa gwamnan Zamfara sammaci kan kujerar shi
- Murna na neman komawa ciki ga 'yan jam'iyyar PDP na jihar Zamfara, yayin da aka aikawa gwamnan jihar sammaci
- Wani koke da dan takarar gwamnan jihar Zamfara a jam'iyyar PDP ya kai kotun koli, inda ya zargi jam'iyyar PDP ta jihar da tsayar da dan takara ba tare da bin ka'ida ba
- Yanzu dai kotun kolin ta aikawa gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammad Nasiha, jam'iyyar PDP da kuma hukumar INEC sammaci
Bisa dukkan alamu murna na neman komawa ciki a jihar Zamfara, musamman ga gwamnan jihar Alhaji Bello Muhammad Matawalle.
Wata takarda da Mujallar Duniya ta samu daga gurin Daraktan Yada Labarai na dan takarar jam'iyyar APC ta jihar Zamfara, Al-Mansoor Gasau, ta bayyana cewa kotun koli ta aikawa gwamnan jihar Bello Matawalle sammaci, da Sanata Hassan Muhammad Nasiha, uwar jam'iyyar PDP ta kasa, da kuma hukumar INEC ta kasa mai zaman kanta.
Ya ce dan takarar jam'iyyar PDP na jihar ne, Dakta Ibrahim Shehu Bakauye ya kai wannan koken ga kotun.
KU KARANTA: Wata Sabuwa: Ba Almajiranci zamu hana ba, zamu zamanantar da makarantun allo ne - Shugaba Buhari
Ya bayyana cewa suna zargin jam'iyyar PDP da fitar da dan takara ba tare da bin ka'ida ba, kamar yadda hukumar INEC ta zargi jam'iyyar APC ta jihar kwanakin baya.
Ga sakon da Al-Mansoor ya aika a kasa:
"Kotun koli dake zaune a babban birnin tarayya ta aikewa shugabannin jam'iyyar PDP na jihar Zamfara da sammaci, a cigaba da sauraron karar da dan takarar kujerar gwamnan karkashin jam'iyyar PDP, Dr. Ibrahim Shehu Bakauye Gusau ya shigar a yau.
"Inda yake zargin jam'iyyar PDP ta jihar Zamfara da zama a gidan wani mutumi ta fitar da 'yan takarar ba tare da bin ka'idar da jam'iyyar PDP ta tsara ba," in ji Al-Mansoor.
Idan ba a manta ba kotu ta kwace kujerar gwamnan jihar ne daga gurin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC ta bai wa gwamnan jihar na yanzu, wanda yake dan jam'iyyar PDP. Inda kotun ta yi zargin cewa jam'iyyar APC ba ta gabatar da zaben fidda gwani ba a jihar.
Haka kuma jam'iyyar PDP ta jihar tana zargin tsohon gwamnan jihar da yin sama da fadi da wasu biliyoyin kudi, inda shi kuma gwamnan ya fito ya bayyana cewa bai bar bashin ko taro a jihar ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng