Cika alkawari: El-Rufai ya kaiwa Sarkin Gombe ziyarar ban gajiya (Hotuna)
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya kai ziyarar ban girma fadar Sarkin Gombe, Mai martaba Abubakar Shehu-Abubakar a yau Asabar 29 ga watan Yuni.
El-Rufai ya ziyarci fadar sarkin ne tare da takwararsa na jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya.
Tun a watan Disambar 2017 na El-Rufai ya dau alkawarin kai wa Sarkin Gombe ziyarar ban girma saboda muhimmiyar gudunmawa da ya bayar yayin bikin Durbar na cikar jihar Kaduna shekara 100 da kafuwa da aka gudanar a 2017.
Gwamnan ya yi alkawarin kaiwa Sarkin ziyara ne saboda gudunmawar da ya bayar lokacin bikin Durbar da akayi na murnar cika shekara 100 da kafa jihar Kaduna da aka gudanar a Disambar 2017.
Sarkin na Gombe na cikin sarakunan da suka hallarci taron da aka gudanar mai kayatarwa.
Ga hotunan yadda ziyarar ta kasance.
DUBA WANNAN: CBN za ta rage yawan kudaden da ke kewayawa a Najeriya, ta bayar da dalili
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng