Allah Sarki: Yadda 'yan uwana suka dinga cin zarafi na saboda munin da Allah yayi mini - Krepin Diata

Allah Sarki: Yadda 'yan uwana suka dinga cin zarafi na saboda munin da Allah yayi mini - Krepin Diata

- Wani dan wasan kwallon kafa na kasar Senegal ya koka da irin yadda aka dinga ci masa mutunci a filin wasa

- Dan wasan ya ce bai ji dadi ba ko kadan ganin yadda 'yan uwansa 'yan Afirka suka dinga zagin shi da cin zarafin sa saboda launin fatarsa

- Ya ce ya godewa Allah da yayi shi lafiyayye ba mai tawaya ba, kuma ya san Allah kadai shine gatan sa

Dan wasan kwallon kafa na kasar Senegal, Krepin Diatta ya bayyana yadda ciwon rai da bakin cikin rayuwa ya isheshi lokacin da mutane suka dinga zagin shi suna ci masa mutunci saboda irin halittar da Allah yayi masa.

Dan wasan ya ce: "Na yi matukar bakin ciki dana ga wasu 'yan uwana 'yan Afirka suna tsokana ta.

"Ina mutukar kokari, na kuma sadaukar da rayuwa ta domin ganin na kare martabar nahiyata ta Afirka, amma mutane suka dinga yi mini dariya, zagi, cin zarafi da kuma aibata halitta ta.

KU KARANTA: Siyasar jihar Kano: Bala'in da ya kunno kai jihar Kano bayan kammala zaben 2019 - Hon. Zulyadaini

"Ni da nake tsananin ganin mun samu nasara, kuma nake goyon bayan yankina, amma zagi shine sakamakon dana samu.

"Ina godewa masoyana da suka nuna soyayya a gareni, kuma Allah shi kadai ne gatana, sannan ina gode masa da yayi ni lafiyayye ba mai tawaya ba.

"Dariyar da kuke yi mini babu abinda za ta canja a rayuwata, sannan ina tunatar da ku cewa kuma duka 'yan Afirka ne tamkar ni," in ji Krepin Diatta.

Satin da ya gabata ne dai aka fara gabatar da wasan kwallon kafa na nahiyar Afirka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng