Yabon gwani ya zama dole: Ayyuka guda 20 da IBB yayi wadanda har yanzu ake cin moriyarsu

Yabon gwani ya zama dole: Ayyuka guda 20 da IBB yayi wadanda har yanzu ake cin moriyarsu

- Tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi ayyuka bila adadin a kasar nan

- Cikin ayyukan tsohon shugaban kasar hadda gina birnin Abuja inda ya mayar da shi babban birnin tarayyar Najeriya

- Sannan shine ya gina babbar hanyar da ta dauko daga Kano zuwa Abuja

Duk da irin yadda mutane suke yi masa kallon hadarin kaji, tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, shine jigo na wasu manyan ayyuka da kasar nan take ji dasu.

Tsohon shugaban kasar yayi ayyuka bila adadin a lokacin da yayi mulkin soja, ciki kuwa harda gina birnin Abuja, inda ya mai da ita babban birnin tarayyar Najeriya.

Mun yi kokari mun binciko muku wasu muhimman ayyuka da tsohon shugaban kasar yayi a lokacin da yayi mulki, wadanda har yanzu al'ummar Najeriya ke cin moriyarsu.

KU KARANTA: Wargi wuri yaka samu: An kama wani dan majalisa, bayan yayi wani mummunan furuci akan bakin haure

Ga jerin ayyukan a kasa:

1. Shine yayi babbar hanyar Kano zuwa Kaduna.

2. Sannan ya kara ta daga Kaduna zuwa Abuja.

3. Shine yayi makarantar koyar da aikin dan sanda ta Wudil wato (Police Academy Wudil).

4. Shine ya kafa hukumar NAFDAC.

5. Shine kuma ya samar da hukumar yaki da miyagun kwayoyi (NDLEA).

6. Shine ya samar da hukumar yaki da hadura ta kasa (FRSC).

7. Shi yayi asibitin kunne na Kaduna (National Ear Care Center Kaduna).

8. Shi yayi gadar Main Land Bridge dake jihar Legas.

9. Shi ya gina filin jirgin sama na jihar Katsina.

10. Shi ya kafa cibiyar yaki da jahilci ta (National Nomadic Education).

11. Shi ya gina filin jirgin sama na babban birnin tarayya Abuja.

12. Shi ya gina jami'ar Abuja.

13. Shi ya gina jami'ar tarayya ta jihar Ondo.

14. Shi ya gina jami'ar tarayya ta jihar Benue.

15. Shi ya gina jami'ar tarayya ta Abekuta.

16. Shine ya gina dam din Bagauda dake jihar Kano.

17. Shine yayi dam din Challawa dake jihar Kano.

18. Shi yayi babbar Sakateriya ta tarayya dake Kaduna.

19. Shi ya gina kamfanin takin zamani dake Fatakwal.

20. Shi ya gina matatar man fetur ta Warri.

21. Sannan shine ya gina babban masallacin juma'a na birnin tarayya Abuja.

Wannan kadan ne daga cikin ayyukan da tsohon shugaban kasar yayi a kasar nan wadanda har yanzu ake cin moriyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel