Allah wadan naka ya lalace: Ina sayarwa da 'yan ta'adda bindiga N30,000, harsashi kuma N700 - In ji Ayuba

Allah wadan naka ya lalace: Ina sayarwa da 'yan ta'adda bindiga N30,000, harsashi kuma N700 - In ji Ayuba

- Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta yi nasarar cafke wani mutumi mai safarar bindigogi da harsashi ga 'yan ta'adda

- Rundunar ta yiwa mutumin tambayoyi a lokacin da take gabatar da bincike akan shi, inda aka dauki bidiyon lokacin da ake yi masa tambayar nawa yake sayar da bindigogin nasa

- Mutumin ya bayyana cewa akwai ta N200,000 da kuma ta N30,000, sannan kuma yana sayar da harsashi N700 kowanne guda daya

Wani sumame da rundunar 'yan sanda ta jihar Neja ta kai, ta kama wani dillali dake sayarwa 'yan fashi da masu garkuwa da mutane bindigogi da harsashi.

Jami'an 'yan sandan sunyi nasarar kama dallalin wanda ya bayyana sunansa da Ayuba Manta Biyam dan asalin jihar Filato, wanda yake addinin kirista, akan hanyarsa da yake kokarin safarar bindigogi da harsashi zuwa ga 'yan ta'addar.

KU KARANTA: Kwadayi mabudin wahala: Yawancin 'yan mata na soyayya ne saboda neman abin sakawa a bakin salatin su - Bincike

A wani bidiyo da jami'in 'yan sanda DSP Hassan Gimba yake yiwa wanda ake zargin tambayoyi, a lokacin da suke bincikar shi, Ayuba ya bayyanawa jami'in yadda yake sayar da bindiga da harsashin.

Jaridar Dabo FM ce ta binciko bidiyon, inda Ayuba yake amsa tambayar nawa yake saidawa 'yan ta'addar bindigar da harsashin.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa akwai bindiga 'yar N200,000 da kuma 'yar N30,000, sannan kuma yana sayar da harsashi N700 kowanne guda daya.

Ayuba ya bayyana cewa yana sayo harsashin ne akan N500 a gurin wani maigidansa, inda shi kuma yake sayar dashi akan N700 domin ya samu ribar 200 akai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel