'Yan bindiga sun hallaka mutane 18 a jihar Sokoto

'Yan bindiga sun hallaka mutane 18 a jihar Sokoto

Wasu 'yan binda da ba a san ko wu waye ba sun kai wani hari tare da kashe mutane 18 a wani kauye da ke gabashin jihar Sokoto a ranar Litinin da daddare.

Sashen Hausa na BBC, da ya wallafa labarin, ya ce wani basarake daga yankin ya shaida wa wakilinsu cewar an kai harin ne a kauyen Malafaru da ke karkashin karamar hukumar Goronyo.

Harin na zuwa ne a cikin kasa da makonni biyu bayan wasu 'yan bindigar sun kashe fiye da mutane 10 a wani hari da suka kai karamar hukumar Rabah da ke gabashin jihar Sokoto.

Jihar Sokoto na makwabtaka da jihar Zamfa mai fama da rigingimun barayin shanu da suka rikide suka koma rikicin 'yan bindiga. 'Yan bindiga sun hallaka dubban mutane a rikicin da jihar ke fama da shi tun shekarar 2011.

A ranar Litinin din ne dakarun sojin Najeriya da ke aiki a karkashin rundunar atisayen ofireshon HARBIN KUNAMA sun gudanar da wani atisaye a jihar Sokoto da kewaye inda suka samu nasarar kama wasu 'yan leken 'yan bindiga a jihar.

DUBA WANNAN: Kungiya ta nemi Buhari ya kwace mukamin da ya bawa Naja'atu a gwamnatinsa

A wata sanar wa da mukaddashin kakakin rundunar soji ta kasa, Kanal Sagir Musa, ya fitar, ya ce dakarun soji sun kama 'yan leken asirin ne a yankin kauyen Damboa da kasuwar Burkusuma, dukkansu a karkashin karamar hukumar Sabon Birni.

Ya bayyana cewar dakarun soji sun samu nasarar kama 'yan leken asirin bayan samun sahihan bayanan sirri a kan al'amuransu da mu'amalarsu da 'yan bindigar.

Daga cikin wadanda aka din akwai; Mallam Ibrahim - kwararren mai kai wa 'yan bindiga rahoto da kuma karbar kudin fansa amadadinsu, Malam Ashiru Goni - wanda ke wa 'yan bidigar safarar kayan masarufi da kasuwanni zuwa sansaninsu, da kuma Mamman Taratse - wanda shine dillalin da ke sayar da shanun da 'yan bindigar suka sata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel