Gwamna Yahaya ya bawa sarkin Gombe babban mukami a gwamnati

Gwamna Yahaya ya bawa sarkin Gombe babban mukami a gwamnati

Sabon gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya nada sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, a matsayin 'Amirul Hajj' kuma shugaban kwamitin wakilai masu kula da maniyyata aikin Hajji na jihar.

A cewar jawabin da babban mai taimakawa gwamnan jihar a bangaren yada labarai da sanarwa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Litini, ya ce aikin kwamitin da sarkin zai jagoranta shine yin aiki tare da hukumar jin dadi da walwalar alhazai na jihar da kuma ragowar hukumomi masu ruwa da tsaki a harkar aikin Hajjin shekarar 2019.

Kwamitin mai mambobi 11 ya kunshi Barista Muhammad Umar a matsayin mataimakin shugaba, Bala na masarautar Waja, Danjuma Mohammed, Malam Ado Gabanni, Adamu Dokoro, Sheikh Girbo da Sheikh Usman Isah Taliyawa.

Ragowar sun hada da Shreikh Naziru Idrisa Umar, Hajiya Farida Sulaiman, Hajiya Uwani Shuaibu Gara da Saidu Shehu Awak a matsayin sakatarn kwamitin.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin hadiman sanata Ahmed Lawan ya yi murabus

A wani labarin na Legit.ng mai alaka da wannan, kun ji cewar hukumar jin dadi da walwalar alhazai a jihar Jigawa (JSPWB) ta bayyana cewa maniyyata aikin Hajjin shekarar 2019 daga jihar za su biya mafi karancin kudin kujerar zuwa kasar Saudiyya idan aka kwatanta da ragowar jihohin Najeriya.

Jami'in hulda da jama'a na JSPWB, Hashimu Kanya, ne ya sanar da hakan ranar Litinin ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Dutse, ya ce gwamnatin jihar Jigawa ce ta kara rage farashin kujerar Hajjin bana.

Kanya ya bayyana cewa yanzu maniyyata aikin Hajji daga jihar za su biya N1,464,322.12 sabanin tsohon farashin kujerar, miliyan N1.6.

Jami'in hulda da jama'ar ya bayyana cewar maniyyatan da suka riga suka biya kudin babbar kujrera, N1,513,798, za a mayar musu da rarar kudi N49,475.98.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng