Sojoji sun kama Mallam Bawa Gomna, shugaban masu garkuwa da mutane a Katsina, da yaransa 20

Sojoji sun kama Mallam Bawa Gomna, shugaban masu garkuwa da mutane a Katsina, da yaransa 20

A cigaba da yaki da aiyukan 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ragowar aiyukan ta'addanci a jihar Katsina, dakarun rundunar soji ta 17, a karkashin atisayen 'Harbin Kunama III' ta samu nasarar kama shugaban 'yan ta'adda, Mallam Bawa Gomna, tare da yaransa 20.

Gomna da yaransa sun yi kaurin suna wajen sace mutane tare da yin garkuwa da su a yankin kananan hukumomin Batsari, Safana da Jibia, inda dakarun soji su ka kama su yayin wani atisaye a cikin watan Yuni, 2019.

Da ya ke tabbatar da kama kasurgumin dan ta'addar, Kanal Sagir Musa, mukaddashin darektan hulda da jama'a da yada labarai na rundunar soji, ya ce, "mun kama wasu daga cikinsu yayin da suke kan aikata ta'addanci, yayin da wasu muka kama su ta hanyar samun sahihan bayanan sirri.

"Ya kamata mu sanar da jama'a cewa 'yan ta'addar da muka kama da kuma wasu da suka gudu, su ne suka addabi kananan hukumomin Batsari, Safana, Jibia da aiyukan ta'addanci."

DUBA WANNAN: Mata na 3 da yara 11 - Mai garkuwa da mutane ya fadi nasarorin da ya samu

Sanna ya kara da cewa, 'yan bindgar sun amsa da bakinsu cewar suna daga cikin 'yan bindigar da ke satar shanu tare da yin garkuwa da mutane a yankin kananan hukumomin.

Kazalika, ya bayyana cewa yanzu haka suna tattara bayanan 'yan ta'addar kafin daga bisani su mika su zuwa hannun hukumomin da suka dace domin yi musu tambayoyi da kuma gurfanar da su.

Kanal Musa ya bayyana cewar nasarar da rundunar soji ke samu a cikin 'yan kwanakin baya bayan nan sun yi daidai da manufar atisayen 'Harbin Kunama III' domin kawo karshen aiyukan 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel