An ci mutuncin Dabo da aka ba ka Sarkin Kauye – Bayero ya fadawa Sarkin Bichi

An ci mutuncin Dabo da aka ba ka Sarkin Kauye – Bayero ya fadawa Sarkin Bichi

Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa Mai girma Hakimin Kura, Bello Bayero, ya yi kira ga ‘Danuwan sa sabon Sarkin Bichi watau Aminu Ado Beyero ya sauka daga wannan sarauta da ya ke kai.

A wani sakon murya mai tsawon minti 18 da a ka ji Hakimin na Kura ya na jawabi, ya nemi ‘Danuwan sa da ke rike da sarautar kasar Bichi da a ka kirkiro ya ajiye wannan mulki, ya koma Birni.

Bello Bayero wanda yanzu an dakatar da shi daga kan gadon mulki bayan da ya ki yi wa sabon Sarkin Rano mubaya’a, ya ke cewa mutuncin gidan sarautar shi ne Aminu Ado Bayero ya yi murabus.

‘Danuwan sabon Sarkin ya ke cewa ya fi dacewa da Aminu Ado Bayero ya cigaba da yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II biyayya, ya rike sarautar Wamban Kano da su ka gada daga Iyaye da kuma kakanni.

Hakimin ya yi wannan jawabi ne ya na kuka inda ya ce: “A kan gadon sarautar dabo ne Mahafin mu (Ado Bayero) ya shafe shekaru 50 ya na mulki cikin zaman lafiya.

Ya kara da cewa: “Ya koya mana son juna da kauna ba tare da nuna banbanci ba.”

Bello Bayero ya yi mamakin yadda ‘Danuwan sa ya karbi wannan sarauta bayan Baffansa watau Galadima Abbas Sanusi da ‘Dan uwan sa Ciroma Nasiru Bayero sun yi watsi da wannan tayi da aka yi masu.

KU KARANTA: Wata Jami’ar Arewa ta ba Mai martaba Sanusi II babban mukami

Bayero ya ke cewa wannan sarauta da aka yi wa ‘Dan uwan na sa, shiri ne kurum na rusa Daular Usmaniyya da gidan Dabo. A jawabin na sa ya ce:

“Mu ‘yan gidan sarautan Birni ne ba kauye ba. Gidan sarauta mai dinbin tarihi. A maimakon Wambai ya jira ranar da zai mulki Kano, ya gaji Mahaifinsa a kan mulki, sai ya buge da karbar wata karamar sarauta maras asali da tarihi."

Alhaji Bayero ya cigaba da cewa:

“Ba a taba samun Sarki a Bichi ba tun daga zamani Sarki Ibrahim Dabo, Muhammad Bello, Muhammad Tukur, Usman I and Usman II, Muhammad Tukur, Muhammad Sanusi, Sarakuna Abbas, Abbas Maje Karofi, Emir Abdullahi Bayero and Emir Alu Maisango ba su taba sarauta a Bichi ba.”

Alhaji Bello Bayero ya ce:

“Har Mahaifin mu, Ado Bayero bai gaji wata sarauta a Bichi ba.”

‘Danuwan Sarkin Bichin ya ke cewa wadanda ke da hannu wajen yin kaca-kaca da Masarautar Kano su ne: Shugaban APC na Kano watau Abdullahi Abbas, da kuma Aminu Babba Dan-agundi.

Bayero ya ce wadannan ‘yan siyasa da wasun su, su na jin haushin irin alakar da ke tsakanin Muhammadu Sanusi II ne da Iyalin Ado Bayero don haka su ke kokarin ganin sun raba ‘Yanuwan.

Hakimin na Kura ya ce, Isa Pilot ne ya shirya wannan danyen aiki na zuga Wambai ya rabu da Sarki, ya karbi wannan sarauta, ya kuma nemi a binciki Pilot da zargin salwantar da wasu miliyan 500.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel