Yanzu Yanzu: Hukumar Aikin Hajji ta rage kujerar hajjin 2019

Yanzu Yanzu: Hukumar Aikin Hajji ta rage kujerar hajjin 2019

Hukumar Kula Da Aikin Hajji Na Kasa (NAHCON) ta rage kudin kejerun hajji na shekarar 2019.

A sakon da NAHCON ta fitar a daren ranar Asabar, Shugaban sashin hulda da Jama'a, Fatima Sanda Usara ta ce an rage kudin kujerar hajjin ne sakamakon wasu canje-canje da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya tayi kan titunan da 'yan Najeriya za suyi amfani da su a kasar mai tsarki.

Hukumar ta Saudiyya ta ce an samu ragin Riyal 620 wanda ya yi dai-dai da Dalan Amurka 165 wanda ya yi Naira 51, 400 a kudin Najeriya.

DUBA WANNAN: Da duminsa: An kama kwararen mayaki na kasa da kasa cikin 'yan Boko Haram a Borno

Sanarwar ta kara da cewa a yanzu maniyattan Najeriya daga dukkan jihohi da babban birnin tarayya, Abuja da sojoji za su samu ragin N51,170.75.

Hukumar Kula da Alhazan ta Najeriya ta umurci ofisohinta na jihohi da Abuja da Sojoji su sanar da sabon farashin kuma su mayarwa wadanda suka biya kudin kujerun su rarar kudin.

Hukumar ta kuma ce ta kara wa'adin biyan kudin hajjin bana zuwa ranar 15 ga watan Yulin 2019 saboda bukatar mutane suka rika yi.

Hukumar ta NAHCON za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin kammala shirye-shiryen kafin fara jigilar maniyatta a wata mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel