Iran ta tsokalo tsuliyar dodo: Za mu shafe kasar Iran daga duniya - In ji Donald Trump

Iran ta tsokalo tsuliyar dodo: Za mu shafe kasar Iran daga duniya - In ji Donald Trump

- Ana ta samun rashin jituwa tsakanin kasar Amurka da kasar Iran

- Kasar Amurka dai tana zargin kasar Iran da harbo wani jirgin leken asirinta maras matuki

- Ita kuma kasar Iran ta bayyana cewa jirgin ya biyo ta sararin samaniyar ta ne, shine yasa ta harbo shi

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa shi ko kadan baya fatan Allah ya hada su yaki da kasar Iran, amma kuma ya yiwa kasar ta Iran gargadi, inda ya bayyana mata cewa idan har yaki ya hado su to babu makawa za ta shafe ta daga doron kasa.

A lokacin da yake hira da gidan talabijin na NBC a jiya Juma'a, shugaban kasar ya kara yiwa kasar ta Iran maganar cewa kasar Amurka a shirye take domin ta tattauna da ita.

Sai dai kuma shugaban kasar ya bayyana cewa babu yadda za ayi kasarsa ta bari kasar Iran ta samar da makaman nukiliya.

Trump ya sake karin haske akan canja aniyar da yayi ta kai wa kasar ta Iran hari, akan mayar da martani kan harbo jirgin leken asirin kasar Amurka da kasar Iran ta yi a cikin makon nan, shugaban kasar yace an bayyana mishi cewa mutane 150 na iya mutuwa sanadiyyar harin.

KU KARANTA: Kunji ita kuma: Wallahi ba zan iya auren saurayin da ba zai saka mukullin mota a kayan aurena ba - In ji wata budurwa

"Bana so ayi haka, ban tunanin hakan ya dace," in ji Trump.

Kasar iran din dai ta bayyana cewa jirgin kasar Amurka din maras matuki ya kutso sararin samaniyarta ne a safiyar ranar Alhamis dinnan da ta gabata.

Sai dai kuma kasar Amurka ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa kasar ta Iran ta harbo jirgin nata ne a sararin samaniyar kasa da kasa.

Ana dai cigaba da samun kace-nace tsakanin kasar Iran da kasar ta Amurka, inda kasar Amurka take zargin kasar Iran da kaiwa wasu manyan jiragen ruwanta hari wadanda suke da danyen mai, a yankin gabas ta tsakiya.

Haka kuma kasar Iran ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba zata fara kera makamin nukiliya, fiye da yadda dokokin kasa da kasa suka amince mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel