Allah jikan maza: Shugabannin Afirka 22 da aka yi musu kisan gilla suna kan mulki daga shekarar 1963 zuwa yau

Allah jikan maza: Shugabannin Afirka 22 da aka yi musu kisan gilla suna kan mulki daga shekarar 1963 zuwa yau

- Mun binciko muku jadawalin shugabbanin Afirka guda 22 da aka yi musu kisan gilla a lokacin da suke ganiyar cin mulkin su

- Sannan rahotanni sun nuna kasar Faransa ce ke hada tuggun kisan da yawa daga cikin shugabannin

- Shugaban kasa da aka kashe na kwana-kwanan nan dai shine, shugaban kasar Libya, Mouammar Gaddafim wanda aka kashe a shekarar 2011

Wani rahoto ya binciko wasu shugabannin kasashen Afirka guda 22 da aka yi musu kisan gilla lokacin da suke kan karagar mulki daga shekarar 1963 zuwa yanzu.

Haka kuma binciken ya dora zargin yadda kasar Faransa ta hada dukkanin tuggun yadda za ayi wannan ta'asar, inda ta dinga hada baki da wasu manyan 'yan Afirka wadanda basu kishin yankin.

Ga jerin sunaye da shekarun da aka kashe wadannan shugabannin kasashen Afirka a lokacin da suke kan karagar mulki:

1. Shugaban kasar Togo, Mista Sylbanus Olympio, an kashe shi a shekarar 1963.

2. Shugaban kasar Najeriya, John Aguiyi Ironsi, an kashe shi a shekarar 1966.

3. Shugaban kasar Somaliya, Abdirachud-Ali Shermake, an kashe shi a shekarar 1969.

4. Shugaban kasar Zanzibar, Abeid Amani Karume, an kashe shi a shekarar 1972.

5. Shugaban kasar Madagascar, Richard Batsimandraba, an kashe shi a shekarar 1975.

6. Shugaban kasar Chadi, Mista Francois Ngarata Tombalbaye, shi ma an kashe shi a shekarar 1975.

7. Shugaban kasar Najeriya, Janar Murtala Ramat Mohammed, an kashe shi a shekarar 1976.

8. Shugaban kasar Congo, Marien Ngouabi, an kashe shi a shekarar 1977.

9. Shugaban kasar Ethiopia, Mista Teferi Bante, shi ma an kashe shi a shekarar 1977.

10. Shugaban kasar Egypt, Anour El-Sadate, an kashe shi a shekarar 1981.

11. Shugaban kasar Liberia, Mista William Rechard Tolbert, shi ma an kashe shi a shekarar 1981.

KU KARANTA: Kunji wani bala'in kuma: An haramta masallatai da tsayar da gemu a kasar China

12. Shugaban kasar Burkina Faso, Mista Thomas Sankara, an kashe shi a shekarar 1987.

13. Shugaban kasar Comoros, Ahmed Abdallah, an kashe shi a shekarar 1989.

14. Shugaban kasar Liberia, Mista Samuel Kanyo Doe, shi ma an kashe shi a shekarar 1989.

15. Shugaban kasar Aljeria, Mohammed Boudiaf, an kashe shi a shekarar 1992.

16. Shugaban kasar Burundi, Mista Mechoir Ndadaye, an kashe shi a shekarar 1993.

17. Haka kuma shekarar 1994 an sake kashe wani shugaban kasar Burundi, Mista Cyprien Ntaryamira.

18. Shugaban kasar Rwanda, Mista Jubenal Habyrimana, shi ma an kashe shi a shekarar 1994.

19. Shugaban kasar Nijar, Ibrahim Barre Mainasara, an kashe shi a shekarar 1999.

20. Shugaban kasar Congo, Mista Laurent Desired Kabila, an kashe shi a shekarar 2001.

21. Shugaban kasar Guinea-Bissau, Mista Joao Bernardo, an kashe shi a shekarar 2009.

22. Shugaban kasar Libya, Mouammar Ghaddafi, an kashe shi a shekarar 2011.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng