Tirkashi: Dumu-dumu na iske mahaifiyata na zina da limamin mu a cikin gidanmu - Wata budurwa ta koka

Tirkashi: Dumu-dumu na iske mahaifiyata na zina da limamin mu a cikin gidanmu - Wata budurwa ta koka

- Wata matashiyar budurwa ta nemi taimakon wata mata akan wani hali da ta shiga jim kadan bayan komawarta gida

- Budurwar ta je ta iske mahaifiyarta cikin gidansu tare da limamin cocinsu, suna aikata zina

- Budurwar ta bayyana cewa ba ta taba ganin munafiki irin limamin na su ba, domin kullum bashi da aiki a coci idan ba ya dinga yi musu wa'azi cewa zina babu kyau ba, sai gashi yau ta kamasu dumu-dumu tare da da mahaifiyarta

Wata kwararriya a fannin zamantakewar ma'aurata, Joro Olumofin, ta bada labarin wata matashiyar budurwa, wacce ta bayyana cewa ta shiga gidansu ta iske limamin cocinsu tare da mahaifiyarta suna zina a cikin gidansu.

A cewar budurwar, ta ce ta dawo gida da rana, kawai sai ta iske mahaifiyarta da limamin cocinsu suna holewa a cikin gidansu. Budurwar ta kara da cewa kawai ta fita ta bar gidan ne saboda bata san me zata ce ba a wannan lokacin.

Budurwar a karshe ta yi tambaya akan, shin yana da kyau mahaifiyarta ta kawo kato har cikin gidansu ko kuwa babu?

KU KARANTA: Zagin Ganduje: Kotu ta tisa keyar mawakin Kwankwasiyya zuwa gidan yari

Ga abinda budurwar ta sanya a shafinta na sada zumunta:

"Dan Allah ina neman taimakon shawarwarin ku. Na dawo gida da rana, kawai sai na iske mahaifiyata da limanin cocin mu suna zina aa tsakar gidanmu, dole ya sanya ni ficewa daga gidan saboda ban san me zance ba a wannan lokacin.

"Shin yana da kyau ma ta dinga kawo kato har cikin gidanmu, kuma shima limamin namu munafiki ne, shine mutumin da yake yi mana wa'azi cewa zina babu kyau a koda yaushe. Gaskiya kai na ya daure na rasa yadda zanyi," in ji budurwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng