Salatul Ga’ib: Malamai sun shiryawa Morsi sallah a Bauchi da Sokoto

Salatul Ga’ib: Malamai sun shiryawa Morsi sallah a Bauchi da Sokoto

A Ranar Litinin watau 17 ga Watan Yuni, 2019, tsohon shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi ya cika. Rasuwan tsohon shugaban kasar wanda ya ke tsare a gidan kurkuku ya girgiza Duniya.

An bizne Mohammed Morsi ne a Ranar Talata, 18 na Yunin 2019 a cikin babban birnin Cairo na kasar Misra. Manyan kungiyoyin Duniya sun nemi a gano abin da ya kashe tsohon shugaban kasar.

A Najeriya an samu mutane da-dama da su ka yi jimamin mutuwar Mohammed Morsi inda har a ka rika yi masa sallar gawa. A Ranar Talata an samu wadanda su ka yi wa Morsi sallar jana’iza a Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga BBC Hausa, an yi wa Marigayin sallar ga’ib a wata kwalejin ilmi ta Nana Asmau da ke cikin Garin Sokoto. An yi masa sallar ne a Ranar Talatan da aka bizne sa a Masar.

KU KARANTA: Iran ta baro wani jirgin Amurka a sararin samaniya

Haka kuma mun samu labari cewa an shirya yin wata sallar jana’izar ta Mohammed Morsi a jihar Bauchi. An shirya wannan sallah ne a jami’ar fasaha ta tarayya ta Abubakar Tafewa da ke Garin Bauchi.

Babban Malami Dr. Mansur Isa Yelwa, wanda shi ne Limamin masallacin ATBU na Bauchi ya bada wannan sanarwa kamar yadda mu ka samu labari. An shirya wannan sallah ne da karfe 1:00 na Yau dinnan.

A wajen Najeriya, an samu dubban jama’a da su ka yi wa tsohon shugaban farar hular sallar musamman a babban masallacin Garin Istanbul. Shugaban Turkiyya, Recap Erdogan ya halarci jana’izar.

Sai dai duk da wannan, a Garin Cairo inda a ka bizne tsohon shugaban, gwamnati ba ta bada dama a halarci sallar da aka yi wa Morsi ba, duk da rokon da Iyalin Mamacin su kayi na a bizne sa a Garinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel