Akwai alamar tambaya a satifiket din Masari – inji Lauyan Lado ‘Danmarke

Akwai alamar tambaya a satifiket din Masari – inji Lauyan Lado ‘Danmarke

‘Dan takarar gwamnan Katsina a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Garba Yakubu Lado, ya bayyana cewa gwamna mai-ci Aminu Masari bai da satifiket da ke nuna cewa ya kammala makaranta.

Sanata Yakubu Lado ya fadawa manema labarai cewa gwamna Aminu Masari bai da takardar shaida da ke nuna cewa ya yi sakandare, sai dai wata takarda ta “To Whom It May Concern.”

‘Dan takarar gwamnan ya fadawa ‘yan jarida wannan ne bayan wani zama da kotun da ke sauraron karar zaben jihar Katsina ta yi. Lado ya yi magana ne ta bakin Lauyansa, Gordy Uche.

Gordy Uche SAN ya kuma bankado batun shekarun gwamnan inda ya ce Mahaifinsa (Umaru Bello) ya taba cike masa takarda da sunan cewa an haife sa ne a Ranar 29 ga Watan Mayun 1950.

KU KARANTA: PDP ta fadawa Kotun zabe cewa Gwamnan Katsina bai yi karatu ba

A lokacin da Mahaifin gwamnan ya cike wannan takarda a cikin 2001, shi kan-sa ya na da shekaru 51 a Duniya. Hakan na nufin yanzu shekarun sa 69 watau daidai da na ‘dan sa Gwamna.

Daga cikin sauran hujjojin da Garba Lado ya gabatar a gaban kotu shi ne zargin rashin sahihancin diflomar gwamnan da kuma kwan-gaba-kwan-baya wajen jerin sunayen da ya ke amfani da su.

Lauyoyin gwamnan na APC sun maidawa PDP martani ta bakin Ernest Obanadike, wanda ya bayyana cewa wanda a ke tuhuma ya na da duk wasu takardun da a ke bukata na tsayawa takara.

An yi wannan ne a farkon makon nan inda yanzu shugaban kotun da ke sauraron wannan kara watau Mai shari’a Hadiza Jos ta ce za a cigaba da zama domin sauraron karar a yau 20 ga Yuni.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel