Gaskiyar abinda ke tsakanina da Rahama Sadau – Yaseen Auwal

Gaskiyar abinda ke tsakanina da Rahama Sadau – Yaseen Auwal

- Babban darakta a kamfanin Kannywood, Yaseen Auwal, ya bayyana abinda ke tsakanisa da fittaciyar jarumar fim, Rahama Sadau

- Ana dai ta yada jita-jitar cewa akwai alaka ta soyayya a tsakanin daraktan da jaruma Rahama Sadau

- Yace babu wata alaka ta soyayya a tsakaninsu, kawai dai shi ya kawo ta harkar fim ya kuma fara sanya ta a fim

Babban darakta a kamfanin Kannywood, kuma Shugaban kamfani shirya fina-finai a UK Entertainment, Yaseen Auwal, ya bayyana abinda ke tsakanisa da fittaciyar jarumar fim, Rahama Sadau.

Ana dai ta yada jita-jitar cewa akwai alaka ta soyayya a tsakanin daraktan da jaruma Rahama Sadau.

Sai dai jarumin ya karyata hakan inda ya bayyana cewa ko kadan babu alaka ta soyayya a tsakaninsa da jarumar.

Auwal ya bayyana cewa shine silar zuwan Rahama masana’antar fim domin shine ya fara kawota masana’antar sannan ya fara sanya ta a fina-finai.

An tattaro inda jarumin ke cewa: “Soyayya tsakanina da Rahama Sadau babu ko kadan. Ni na kawo Rahama Sadau Kannywood, ni na fara sa ta a fim, tun daga lokacin da na fara sa ta a fim muke da kyakkyawar alaka, har kawo yanzu kuma babu wani abu zan ce ta yi mini na rashin kyautatawa. Tana mutunta ni, tana ba ni daraja, ina zama da ita sosai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a kamfanin NNPC, Kyari ya zama manajan darakta

“Muna zama mu yi shawara, don yanzu kafin in fara waya da kai ma na dade ina magana da ita ta waya, duk da cewa tana Saudiyya. Alakar da ke tsakaninmu mutane suke gani kamar soyayya ce a tsakaninmu, amma ba haka ba ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel