Mun cancanci a bamu kujerar minista – Kannywood ga Buhari

Mun cancanci a bamu kujerar minista – Kannywood ga Buhari

- Manajan Darakta na kamfanin Abnur Entertainment, Alhaji AbdurRahman Muhammad, ya bayar da dalilan da yasa masana’antar Kannywood ta cancanci samun mukamin minista

- Abdul Amart yace masana'antar ta shir fina-finan Hausa taka gagarumin rawar gani wajen nasarar zaben shugaba Buhari a 2015 da 2019

- Don haka yace lokaci yayi da ya kamata Buhari ya basu mukamin Minista da kuma gina gidajen kallo a fadin jihohin arewa 19

Babban furodusa na Kannywood kuma Manajan Darakta na kamfanin Entertainment, Alhaji AbdurRahman Muhammad, ya bayar da dalilan da yasa masana’antar shirya fina-finan Hausa ta cancanci samun mukamin minista daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Furodusan wanda aka fi sani da Abdul Amart Mai Kwashewa wanda yayi magana a ranar Litinin yayi bayanin cewa, muhimmin rawar ganin da mawaka, da yan fim din Kannywood suka taka wajen kamfen din shugaba Buhari a 2015 da 2019 yasa masana’antar ta cancanci a saka mata da mukamin minista.

Abdul Amart wanda ya jagoranci jaruman Kannywood wajen yiwa Buhari kamfen a lungu da sakon yankin arewacin Naajeriya yace rawar ganin da suka taka yasa yan Najeriya da dama sun zabi Buhari a zabukan 2015 da 2019.

Yace: “Mun taka muhimman rawar gani wajen daura Buhari a mulki, mun ja hankalin masu kallonmu, sannan a bangarenmu mun sa yan Najeriya da dama sun zabi Buhari a zaben Shugaban kasa na 2015 da 2019.

“Idan kun lura sosai, Kannywood bata yi wa Buhari kamfen ba a 2003, 2007 da 2011 sannan me ya faru? Ya fadi zabe, mun san cewa ya ci zabe a 2015 da 2019 amma rawar ganin da muka taka ma ya taimaka wajen sama masa miliyoyin kuri’u, saboda mun shirya masa wakoki masu dadi, mun yi masa kamfen din gida-gida."

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya kafa kwamiti domin sake duba rahoton hukumar yaki da rashawa kan Sanusi

Yace a 2015 Buhari bai yiwa Kannywood komai ba amma yanzu ne lokaci da ya dace ya basu mukamin minista. Sannan kuma yace suna so a gida gidajen kallo a fadin jihohi 19 na arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel