IBB, Ironsi, za su halarci taron kaddamar da wani littafi da Sojin Najeriya ya rubuta

IBB, Ironsi, za su halarci taron kaddamar da wani littafi da Sojin Najeriya ya rubuta

Mun ji cewa a na sa rai cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), da Thomas Agu-Iyi Ironsi za su halarci wani taron kaddamar da littafi a Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar The Cable a Ranar Litinin, 16 ga Watan Yuni, 2019, tsohon shugaban kasar na lokacin soji watau IBB da tsohon Ministan tsaron za su halarci bikin.

Aboyami Balogun shi ne ya wallafa wannan sabon littafi da za a kaddamar a tsakiyar makon nan. Balogun ya rubuta wannan littafi ne a kan yakin da Sojojin Najeriya su ka yi a kasar Sierra Leone.

Kungiyar "Green Heroes Foundation" mai zaman kan-ta ce ta shirya wannan taro na kaddamar da littafin da za ayi tare da gudumuwar cibiyar “Africa Centre for Strategic Studies” ta Nahiyar.

KU KARANTA: Buhari da Gwamnan Legas sun yi wani kus-kus a Aso Villa

Wannan Marubucin watau Abayomi Balogun, ya bayyana cewa wannan littafi zai yi maganan tarihi tare da kawo irin darasin da ya dauka wajen yake-yake da kuma sha’anin tsaron kasa.

Har wa yau wannan littafi zai yi magana a kan matsalar nan da ake kira PTSD da sojoji ke fuskanta bayan sun shiga gumurzu a dalilin cin karo da gawa da kuma yawan ganin mutuwa tsirara.

Za a kaddamar da wannan littafi mai suna “Nigerian Air War in Sierra Leone, from the Cockpit of Aggressor 08, a Ranar Laraba, 19 ga Watan Yunin 2019”, a cikin babban birnin tarayya da ke Abuja.

Badamasi Babangida da tsohon Ministan kuma yaron Marigayi JTU Ironsi, su na cikin wadanda aka kira su halarci bikin kaddamar wannan littafi da wani tsohon sojan sama ya rubuta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel