Zaben fitar da gwanin gwamna ya raba-kan Shugabannin APC a Jihar Kogi
Wasu daga cikin manyan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kogi sun yi kira ga uwar-jam’iyya ta sa baki wajen ganin an yi amfani da tsarin kato-bayan-kato wajen tsaida ‘dan takarar gwamna a APC.
Kamar yadda labari ya zo mana a jiya Ranar Litinin, 17 ga Watan Yunin 2019, wasu daga cikin masu fada-a ji a cikin APC su na so jam’iyyar ta yi ‘yan tinke wajen fito da wanda zai rike tutar gwamna.
Wadannan kusoshi na jam’iyya sun yi wannan magana ne a lokacin da aka shirya wani taro na masu neman kujerar gwamna a jihar inda ‘yan takara 17 cikin 20 da ake da su a jihar su ka halarta a Abuja.
Sanata Alex Kadiri ta bayyana cewa:
“Mun shirya wannan taro ne bayan samun labari cewa wani haramtaccen kwamiti da aka nada na Yaran Yahaya Bello su na kokarin ganin an yi amfani da Wakilan jam’iyya wurin tsaida ‘dan takara.”
KU KARANTA: Yadda ‘Yan takaran APC a Kudu su ka rasa kujeru saboda Buhari
Sanata Kadiri ya kara jaddada:
“Babu shakka cewa an samu baraka a cikin-gidan APC a jihar Kogi, saboda wannan baraka ne mu ka tafi kotu. Har yanzu wannan magana ta na gaban shari’a, sai dai ba mu iya janyo shari’ar kamar yadda aka yi a jihar Zamfara ba.”
Kadiri a madadin sauran manyan jam’iyyar ya kuma cigaba da cewa:
“Yayin da a ke shiryawa zaben fitar da gwani, mu manyan APC da sauran ‘yan takarar gwamna 20 na APC ba mu tare da shirin da Yahaya Bello ya ke yi na tafka magudi wajen samun tikitin jam’iyya.”
“Dole a yi amfani da tsarin zabe na kato-bayan-kato inda kowane ‘Dan APC daga cikin kananan hukumomin jihar zai fito ya zabi ‘dan takarar gwamnan da ya ke so” Inji Sanata Alex Kadiri.
Sanata Kadiri ya kare da cewa su na da labarin yadda Yahaya Bello ya yi watsi da jam’iyya, ganin ya rasa tikitin takara amma APC ta kakaba shi a matsayin gwamna bayan rasuwar Abubakar Audu.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng