Sheikh Gumi: Duk wanda ya sanya hannu akan dokar wa'azi yayi ridda

Sheikh Gumi: Duk wanda ya sanya hannu akan dokar wa'azi yayi ridda

- Shahararren mlamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa duk mutumin da ya bari aka sanya hannu akan dokar gudanar da wa'azi yayi ridda

- Ya ce shi bai ga amfanin wannan dokar ba domin kungiyoyi da yawa basu yadda da gwamnati ba ballantana kuma wata dokar ta

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa bai kamata ba gwamnati ta kawo wata doka ta gyare-gyare akan addini ba tare da ta tuntubi malamai masu ruwa da tsaki a kowanne bangare ba, ma'ana malaman Musulunci dana Kirista.

Malamin ya kara da cewa harkar addini ba harka ce ta siyasa ba, saboda haka bai kamata gwamnati ta kunno wutar rikici ba daga baya kuma tazo tana cewa malamai suyi addu'ar samun zaman lafiya.

A cewar shahararren malamin kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowanne mutumi damar gabatar da addinin da yake so, ba tare da wani ya tsangwame shi ba, maganar bada lasisi babu abinda za ta kawo sai matsaloli. Saboda a halin da ake ciki yanzu akwai kungiyoyi na addini da su bama su yadda da gwamnatin ba ballantana zancen lasisin ta.

KU KARANTA: Zamfara: Duk sarkin da ya bari aka kashe mutum a masarautarsa zan tsige shi - Matawalle

Malamin yayi misali da kungiyar Boko Haram da kungiyar 'yan Shi'a, inda ya ce "Wa ya basu lasisi kafin su fara gabatar da wa'azin su? Amma kuma duk da haka suna da magoya baya masu dumbin yawa a kowanne lungu na kasar nan.

"Amma idan har gwamnati tana yin hakanne da kyakkyawar manufa Allah zai ba ta nasara akan dukkanin abubuwan da take yi, amma matukar ba tana yi saboda Allah bane to sanya hannu a wannan kudiri kamar yin ridda ne, saboda duk wanda ya kange zuwa ga hanyar Allah yayi ridda.

"Sannan a tawa fahimatar gwamnati tayi kuskure matuka wurin gabatar da wannan kudiri, saboda ba haka ake fuskantar kalubale irin wannan ba, kamata yayi a zauna da bangaren malaman addinin Musulunci dana Kirista, domin kowa ya bada tasa gudumawar kafin daga bisani gwamnati ta kai abin ga majalisa, domin mayar dashi doka."

Daga karshe shahararren malamin ya bayyana cewa idan har aka ce za'a saka dokar bada lasisi, wanene zai bai wa wani lasisin? Musulmi ne zai bawa Kirista ko kuwa Kirista ne zai bawa Musulmi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel