Rashin tsaro: Gwamnan Zamfara ya gana da kungiyar Miyetti Allah

Rashin tsaro: Gwamnan Zamfara ya gana da kungiyar Miyetti Allah

-Bello Matawalle ya cigaba da bada himma a bangaren tsaron jihar Zamfara inda ya gana da kungiyar Miyetti Allah.

-A 'yan kwanakin da suka gabata gwamnan ya tattauna da Shugaba Buhari kan matsalar tsaron jihar Zamfara wacce ta dade ta na cima al'ummar jihar tuwo a kwarya.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a ranar Laraba ya gana da jagororin kungiyar Miyetti Allah a wani yunkuri da yake yi na kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar.

Kamfanin dillacin labarai na kasa wato NAN ya ruwaito cewa, ana zargin kungiyar ta Fulani da sa hannu cikin kashe-kashen dake addabar jihar.

KU KARANTA:Babu wanda zai hana mu binciken Sarki Sanusi, inji Hukumar yaki da cin hanci ta Kano

Matawalle ya ce: “ Wannan ganawa ta kasance bisa ganawar da mu kayi da Shugaba Buhari inda ya ce lallai in tabbata na zauna da ire-iren wadannan kungiyoyi domin gano bakin zaren matsalar rashin tsaro a yankinmu.”

“ A cikin kwanakin nan na gana da Shugaba Buhari kan matsalar tsaro da muke fama da ita a jiharmu.”

“ Yayin ganawar da nayi da shugaban kasa, na yi ma shi alkawarin cewa zan zauna da shugabannin kungiyoyi, sarakunan garjiya da kuma hakimai domin warware wannan matsala.”

Matawalle ya cigaba da cewa: “ Samar da tsaro a jihar Zamfara na daya daga cikin kudurorina tun kan na zama gwamna. Ina godiya ga Allah da ya bani damar kasancewa gwamna a halin yanzu.”

“ Kowa ya san Fulani mutanen kirki ne da babu ruwansu da fitina. Sai gashi abinda ke faruwa a Zamfara dama wasu sassan kasarnan ya shafawa Fulani kashin kaji. Kamar yadda na fadi yayin jawabin karbar aiki, lokaci yayi da zamu kawo karshen kashe-kashe a jiharmu, ina nan kan bakata har wa yau.”

Ana shi jawabin kuwa, shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Muhammad Kiruwa ya roki gwamnatin jihar da ta sanya ‘yan sitiri da kuma ‘yan sa kai cikin wannan shiri na yakar ta’addanci da ya sa jihar gaba.

Har ila yau, ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar Zamfara bisa wannan dama da ta basu, inda ya kara da cewa, “kungiyarsu a kullum shirye take ta ba gwamnatin goyon baya domin a cinma nasara a fannin yaki da ta’addanci.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel