Kuma dai: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da wani basarake a Katsina

Kuma dai: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da wani basarake a Katsina

Wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton 'yan bindigan ne sun sace sarkin garin Labo da ke karamar hukumar Batsari na Jihar Katsina a ranar Talata.

A halin yanzu ba a bayyana sunan sarkin kauyen ba da aka ce an sace shi misalin karfe 1 na rana a gonarsa tare da wasu mazauna kauyen kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wasu da suka bayyana abinda ya faru sun ce 'yan bindigan sun kai farmaki gonakin a kan babura suna harbe-harbe kuma cikin wannan hargitsin ne aka sace sarkin kauyen yayin da wasu da ke tare da shi suka tsere.

DUBA WANNAN: An gano yadda aka bawa 'yan majalisa toshiyar baki don zaben Gbajabiamila

Kakakin Rundunar Yan sanda na Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin a yau Laraba.

Ya ce, "Gaskiya ne. A halin yanzu ana kokarin yadda za a ceto shi daga hannun wadanan bata garin. Operation Puff Adder sun amsa kirar da a kayi musu kan harin amma saboda a cikin gonarsa ne abinda ya faru can kusa da dajin Rugu, 'Yan bindigan sun tsere da shi cikin daji kafin 'yan sanda su isa wurin. Muna bin sahunsu domin ganin an ceto shi.

"Rundunar 'yan sanda tana kira ga mazauna garuruwan da ke kusa da dajin su rika yin tawaga idan za su tafi gona kuma su rika sanar da hukumomin tsaro domin samun wanda za su tsare su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel