Waiwaye: Shaida ya bayyana yadda Abiola ya mutu ana daf da sakin sa

Waiwaye: Shaida ya bayyana yadda Abiola ya mutu ana daf da sakin sa

Wani shaida kan yadda rasuwar marigayi MKO Abiola ya mutu ya yi bayyani kan abubuwan da suka faru daf da rasuwar tsohon dan siyasar da aka amince ya lashe zaben shugabancin kasar Najeriya na ranar 12 ga Yuni.

A watan Yulin 1998 harkokin siyasar Najeriya na gudana cikin gaggawa. Bayan rasuwar Janar Sani Abacha, sojoji sun nuna alamar za su mayar da mulki a hannun farar hula a karo na farko tun shekurun 1980s.

Cif Moshood Abiola ya yi ikirarin shine shugaban kasar Najeriya na gaskiya. Shekaru biyar da suka gabata, dukkan alamu sun nuna cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa amma tsohon shugaban kasar mulkin soji, Sani Abacha ya soke zaben kuma ya tsare Abiola a kurkuku.

Bayan rasuwar Abacha, anyi tsamanin za a sako Abiola cikin 'yan kwanaki.

DUBA WANNAN: An gano yadda aka bawa 'yan majalisa toshiyar baki don zaben Gbajabiamila

Tsohon ambasadan Amurka a Najeriya, Thomas Pickering ya jagoranci wata tawaga mai muhimanci domin kai ziyara ga sabon shugaban mulkin soji na wancan lokacin, Janar Abdulsalami Abubakar. Sun isa Najeriya a ranar 6 ga watan Yuli kuma suka gana da shugaban kasar kana suka yi magana kan sakin Cif Abiola.

Thomas Pickering ya bayyana yadda shi da tawagarsa suka shaidawa gwamnati cewa Abiola ya dade a tsare kuma suka bukaci a fara duba yiwuwar sakinsa sai dai a wancan lokacin gwamnatin ta nuna alamar tana son karin lokaci kafin daukan mataki kan lamarin.

Hakan yasa Pickering ya nemi izinin shi da tawagarsa su gana da Cif Abiola wanda a lokacin ya ke tsare a wani gida a Abuja kuma aka amince da bukatar su.

A yayin haduwar su, Pickering ya ce, "Yana cikin koshiyar lafiya ban ga alamar rama a jikinsa sosai ba kuma ya gane ni da sauran 'yan tawaga ta (Susan Rice da William H. Twaddell) da muka shiga gidan. Mun zauna a kujera sannan aka kawo mana shayi kuma dukkan mu muka sha shayin daga cikin butar shayi guda saboda wasu na zargin an saka guba cikin shayin. Amma kafin ya fara shan shayin sa sai ya fara furta wasu maganganu da bamu ganewa kuma kwatsam sai ya ce mana zai shiga ban daki inda ya shafe wasu mintuna kafin ya fito."

Thomas Pickering ya cigaba da cewa, "Bayan ya fito daga ban dakin bai ya zauna a gefen kujera ya ce a nemo masa maganin ciwon jiki sai kuma ya ce yana jin zafi sannan ya tube rigarsa.

"Hakan ya bani mamaki saboda na san shi musulmi ne kuma tube rigarsa a gaban mace alama ce da ke nuna akwai wani abinda ke damun sa.

"Daga nan zai ya fadi a kasa, na duba numfashinsa na gano ba mutuwa ya yi ba. Susan ta kira likita yayin da mu kayi kokarin bashi tallafin da za mu iya amma ba ya iya magana da za a fahimta a wannan lokacin. Dakta Suleiman Wali ya hallara cikin 'yan mintuna sannan ya yi amfani da na'urar gano bugun zuciya ya gwada shi.

Sulaiman Wali ya ce,"Yana da rai amma yana cikin wahala. Daga nan na fara kokarin farfado da shi sannan muka garzaya da shi asibitin gidan shugaban kasa."

Thomas Pickering ya ce, "Dakta Wali ya fito daga dakin tiyata bayan sa'a guda ya ce - munyi iya kokarin mu don ceto ransa amma ba muyi nasara ba sai dai yanzu akwai abu guda biyu da za kuyi min: Mu kira Janar Abubakar mun fada masa abinda ya faru. Sai kuma ya fadi wani abu mai muhimmanci. Ya ce: "Ku yi duk mai yiwuwa ku shawo kan mahukunta asibitin nan ayi gwajin sandin mutuwarsa."

Cif Moshood Abiola ya mutu misalin karfe 4 na yama sakamakon buguwar zuciya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel