Jerin 'yan wasa guda 10 da suka fi kowa daukar albashi mai yawa a duniya

Jerin 'yan wasa guda 10 da suka fi kowa daukar albashi mai yawa a duniya

- Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Lionel Messi shine na farko a jerin sunayen, daga shi sai Christiano Ronaldo sai kuma Neymar

- Da aka hada jimillar kudin ya kai kimanin Pounds biliyan hudu

Jaridar Forbes ta kasar Amurka ta saki jerin sunayen mutanen da ta saba saki kowacce shekara na 'yan wasa guda dari da suka fi daukar albashi mai tsoka a duniya, wanda da aka hada jimillar kudinsu ya kai dala biliyan hudu a wannan shekarar, hakan yasa kudin wannan shekarar ya karu da kashi biyar akan na shekarar da ta gabata.

Wanda ya fi kowa daukar kudi a jerin sunayen shine Lionel Messi, wanda ya fito a na daya a cikin 'yan wasan da suka fi karbar albashi mai yawa, hakan ya sa ya yiwa abokin hamayyarsa Christiano Ronaldo fintinkau.

Dan wasan dan kasar Argentina kuma dan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ya samu 99.8 miliyan Pounds, inda shi kuma dan wasan kwallon kafa na kungiyar Juventus Christiano Ronaldo ya samu 85.7 miliyan Pounds hakan ya bashi damar fitowa a matsayin na biyu a jerin mutanen.

Na ukun su kuma shine dan wasan kwallon kafar nan na kungiyar PSG Neymar, wanda ya samu 82.5 miliyan Pounds.

KU KARANTA: Da duminsa: Yadda aka rabawa 'yan majalisu cin hancin daloli domin su zabi Gbajabiamila

Ga jerin sunayen 'yan wasan guda 10 da kuma yawan kudaden da suke dauka a kasa:

1. Lionel Messi - Kwallon kafa - Naira biliyan 45.9

2. Christiano Ronaldo - Kwallon kafa - Naira biliyan 39.5

3. Neymar - Kwallon kafa - Naira biliyan 38.1

4. Canelo Alvarez - Dambe - Naira biliyan 34

5. Roger Federer - Tennis - Naira biliyan 33.2

6. Russell Wilson - Football - Naira biliyan 32.1

7. Aaron Rodgers - Football - Naira biliyan 32

8. LeBron James - Kwallon kwando - Naira biliyan 32

9. Stephen Curry - Kwallon kwando - Naira biliyan 28.9

10. Kevin Durant - Kwallon kwando - Naira biliyan 23.4

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel