Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 168 ne ke mutuwa a kowacce rana a kasar Yaman

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 168 ne ke mutuwa a kowacce rana a kasar Yaman

- Rahotanni sun nuna cewa mutane bakwai ne ke mutuwa a kowacce sa'a daya a kasar Yaman

- Rashin isashen magunguna da abubuwan kula da kiwon lafiya shine ya jawo hakan

- Rahoton ya nuna cewa iyaye mata da yara kanana su matsalar tafi shafa a kasar

Asusun dake taimakawa kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya sanar da cewa a dukkan sa'a daya a kasar Yaman ana yin asarar mutane 7, inda mahaifiya 1 da Yara 6 suke mutuwa.

Kungiyar ta kuma sanar da cewa kasar ta Yaman ita ce kasa wacce ta fi kowacce talauci a yankin kasashen Gabas ta Tsakiya.

- KU KARANTA: Jerin 'yan wasa guda 10 da suka fi kowa daukar albashi mai yawa a duniya

Bayanin ya bayyana cewa: "Iyaye mata da yara kanana sun fi kowa shiga wannan tashin hankali, duk kuwa da cewa kungiyoyi na bada tallafi suna iya bakin kokarinsu matuka wurin ganin an magance matsalar, kowacce sa'a daya ana samun asarar uwa guda daya da yara kanana guda shida.

A wani bangaren kuma an bayyana cewa kashi 51 cikin dari ne kawai ake iya amfani da shi cikin magunguna a kasar. Magunguna da kayayyakin kiwon lafiya sun yi karanci matuka a kasar.

'Yan Husi sun kwace babban birnin kasar a shekarar 2014, inda a shekarar 2015 aka fara gwabza mummunan yaki tsakaninsu da kasar Saudiyya da kasashe magoya bayanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel