Zaben shugabannin majalisa: Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja (Hotuna)

Zaben shugabannin majalisa: Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja (Hotuna)

Kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a karkashin shugabancin Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, sun yi wata muhimmiyar ganawa dangane da zaben shugabannin majalisar tarayya da za a yi ranar Talata.

Gwamnonin sun gana ne a gidan gwamnatin jihar Kebbi dake Abuja domin tattauna wa a kan yadda zasu tabbatar da cewar 'yan takarar da jam'iyyar APC ta nuna ne suka samu nasara a zaben da za a yi a zauren majalisar wakilai da ta dattijai.

Da yake jawabi bayan kammala taron da aka yi a ranar Lahadi, Bagudu ya bayyana cewar kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ta goyi bayan takarar Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattijai da kuma Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban majalisar wakilai.

Zaben shugabannin majalisa: Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja (Hotuna)

Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja
Source: Twitter

Zaben shugabannin majalisa: Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja (Hotuna)

Gwamnonin APC
Source: Twitter

Zaben shugabannin majalisa: Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja (Hotuna)

Gwamnonin APC yayin taron gaggawa a Abuja
Source: Twitter

Zaben shugabannin majalisa: Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja (Hotuna)

Gwamnonin APC sun yintaron gaggawa a Abuja
Source: Twitter

Lawan zai fafata da Ali Ndume, sanatan jam'iyyar APC daga jihar Borno, yayin da Gbajabiamila zai kara da Honarabul Umar Mohammed Bago, mamba a majalisar wakilai da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar APC daga mazabar Chanchaga a jihar Neja.

DUBA WANNAN: Sabbin ministoci: An leko dalilin da yasa Buhari zai rike wasu ministocinsa 6 a zango na biyu

Tuni shugabancin jam'iyyar APC na kasa da jagoranta, Bola Tinubu, suka bayyana cewar dukkan dan jam'iyyar APC da ba zai goyi bayan 'yan takarar da jam'iyyar ke so ba, yana iya ficewa daga jam'iyyar ba tare da wani bata lokaci.

Saidai hakan bai saka Ndume da Bago janye takararsu ba kuma basu fice daga jam'iyyar APC ba har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel