An kama wani malamin makarantar Allo da ya ke hada kai da Almajiransa suna satar mutane

An kama wani malamin makarantar Allo da ya ke hada kai da Almajiransa suna satar mutane

- An cafke wani malamin makarantar allo da matarsa da 'ya'yansa da kuma almajirai 55 da suke satar mutane

- Bayan haka kuma an kama sama da mutane 20 a yankin gidan malamin da ake tunanin suna da hannu a satar mutanen

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wani malamin addinin Musulunci mai suna Alfa Majid Olore, bayan an gano wani gida da yake satar mutane yana boye a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Jaridar Independent ta bada rahoton an kama Alfa tare da matarsa da 'ya'yansa da kuma sama da Almajiransa 55, wadanda ke zama a Ita Baale a cikin garin Ibadan.

Haka kuma kimanin mutane 20 rundunar 'yan sanda suka kama a yankin Ita Baale.

A cewar wani wanda lamarin ya faru akan idonsa, mutanen da ake zargin an kulle su a ofishin 'yan sanda na Agugu dake garin Ibadan.

KU KARANTA: Matan Ghana sun fi na Najeriya iya soyayya da rikon amana - In ji wani Saurayi

Mutumin ya ce, "Shi dai ya san yaga 'yan sanda sun zo gidan malamin dake unguwar Ita Baale, inda suka kama shi da matarsa da 'ya'yansa da kuma Almajiransa guda 55, sannan kuma an kama wasu mutanen suma a unguwar. Ban san ainahin abinda suka yi ba a lokacin, amma dai naga 'yan sandan na dukan Malamin kamar baza su barshi da rai ba, daga baya suka sanya mishi ankwa."

A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Mista Olugbenga Fadeyi, ya ce har yanzu hukumar tana bincike akan lamarin domin tabbatar da cewa zargin da ake yi gaskiya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel