An ga watan Sallah a wasu garuruwan Najeriya

An ga watan Sallah a wasu garuruwan Najeriya

Rahotonni dake shigo mana daga sassan Nageriya daban-daban na nuni da cewar an ga jaririn watan Shawwal (watan karamar Sallah) a wasu garuruwa kamar haka: Potiskum da Unguru a Jihar Yobe, Daura a Jihar Katsina da Jimeta a jihar Adamawa da Jihar Legas.

Har yanzu ana jiran sanarwa a hukumance daga bakin mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III.

Kafin samun wannan labari, Legit.ng ta sanar da ku cewar ta tabbata gobe Talata take Sallah yayin da sabon jaririn watan Shawwal ya bayyana a kasar Saudiya.

Hakika gobe ne 1 ga watan Shawwal na shekarar Alif dubu daya da dari hudu da arba'in bayan hijirar fiyayyen Halitta daga birnin Makkah zuwa Madinah.

A gobe da ta kasance Talata, 4 ga watan Mayun 2019, za a gudanar da shagulgula na bikin karamar Sallah a kasar Saudiya yayin da jaririn watan Shawwal ya bayyana a Yammacin yau bayan an kai azumi na ashirin tara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel