Likafa ta cigaba: An samu zababben Sanata dan Kwankwasiyya a kasar Gambia

Likafa ta cigaba: An samu zababben Sanata dan Kwankwasiyya a kasar Gambia

Mabiya darikar siyasar Kwankwasiyya dake karkashin jagorancin tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cike da farin ciki biyo naso da manufar darikarsu tayi zuwa wajen Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito a makon data gabata ne aka jiyo Sanata Rabiu Kwankwaso yana bayyana yadda darikar Kwankwasiyya ta samu karbuwa a duk fadin duniya bama cikin Najeriya kadai ba, a cikin wata hira da yayi da manema labaru.

Likafa ta cigaba: An samu zababben Sanata dan Kwankwasiyya a kasar Gambia
Kwankwaso da Billay
Asali: Facebook

KU KARANTA: El-Rufai ya bayyana muhimmin rawar da Buhari ya taka wajen zaben Gbajabiamila

“Kai bama Kano ba, bama Najeriya ba, hatta kasashen waje akwai yan Kwankwasiyya, nan wani yaro daga kasar Gambia yazo karatu Najeriya a jami’ar Obasanjo ta Bells, sai yaga daliban Kano dayawa yace waya turosu aka ce masa Kwankwaso.

“Daga nan ya dauki alwashin sai ya sadu dani, haka ya biyoni har Kaduna bayan mun yi wani taro a Abuja, yace ni yake so na sanya masa hular Kwankwasiyya, kuma na sanya masa hularmu, a yanzu haka yaron ya zama dan majalisa a kasar Gambia, dayake majalisa dayace a kasar, tamkar Sanata yake.” Inji shi.

Likafa ta cigaba: An samu zababben Sanata dan Kwankwasiyya a kasar Gambia
Kwankwaso da Billay
Asali: UGC

A yanzu haka Kwankwaso ya isa kasar Gambia domin ganawa da wannan matashi, inda isarsa filin sauka da tashin jirage na kasar dake Banjul ya samu tarbar Sanata Billay G Tunakara, wanda yayi masa rakiya har zuwa masaukinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng