Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina (Hotuna)

Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina (Hotuna)

Dakarun sojin Najeriya na rundunar atisayen HARBIN KUNAMA III sun yi nasarar kama wasu 'yan bindiga dake satar mutane domin garkuwa da su da kuma aikata fashi da makami.

Rundunar sojin ta kama mutanen ne yayin wani atisaye da ta gudanar a kauyen Sheme da hanyar zuwa dajin Ruwan Godiya da makwabatan kauyaka dake karkashin karamar hukumar Faskari.

A sanarwar da kanal Sagir Musa, mukaddashin darektan yada labaran rundunar soji, ya fitar a shafin rundunar soji dake 'facebook', ya ce dakarun soji sun gudanar da atisaye a kauyen ne bayan samun sahihan bayanan sirri a kan aiyukan 'yan ta'addar da suka addabi kananan hukumomin Funtua da Faskari.

Rundunar soji ta kafa runduna ta musamman tare da tura ta karamar hukumar Faskari domin kawo karshen aiyukan 'yan ta'adda da suka addabi kauyukan karamar hukumar ta Faskari da karamar hukumar Funtua mai makwabataka da ita.

Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina (Hotuna)

Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina
Source: Twitter

Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina
Source: Twitter

Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina (Hotuna)

An kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina
Source: Facebook

Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina (Hotuna)

An kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina
Source: Twitter

Sagir Musa ya bayyana cewar dakarun sojin sun yi nasarar kama wasu 'yan ta'adda guda biyar a kauyen Sheme dake kan hanyar zuwa dajin Ruwan-Godiya tare da bayyana cewar yanzu haka dakarun soji na cigaba da gudanar da atisaye a maboyar 'yan ta'adda dake yankin.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: El-Rufa'a ya yi sabbin nade-nade guda biyar

Ya kara da cewa 'yan ta'addar da aka kama sun bayyana cewar sune ke aikata laifukan fashi da makami tare da satar mutane domin neman kudin fansa. Sun bayyana cewar suna aika mutanen da suka sace zuwa wurin shugabanninsu dake sansaninsu a cikin surkukin dajin Ruwan-Godiya.

"Sakamakon hakan, dakarun soji sun kara kutsa wa cikin dajin Ruwan-Godiya tare da kone sansanin 'yan bindiga yayin da mu ke cigaba da gudanar da atisaye domin farautar ragowar 'yan bindigar," a cewar sa.

Kazalika, ya bukaci jama'a da suke bayar da sahihan bayanai ga rundunar soji a kan duk wani motsin 'yan bindiga da 'yan ta'adda domin daukan matakan gaggawa a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel