Sabon gwamnan Zamfara ya bawa tsohon ministan Jonathan mukami

Sabon gwamnan Zamfara ya bawa tsohon ministan Jonathan mukami

Sabon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya nada tsohon Ministan Kudi a zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, Bashir Yuguda a matsayin mai bashi shawara na musamman.

Gwamnan ya yiwa Yuguda nadin ne tare da wasu mutane shida kamar yadda ya ke dauke cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ayyuka da nade-naden 'yan fadan gwamnati na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ibrahim Suleiman.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

Sauran da aka yiwa nadin mukamman sun hada da sabon sakataren gwamnati, (SSG) Alhaji Bala Bello, Babban mai bayar da shawara na musamman kan harkokin tsaro(SSA)Alhaji Abubakar Dauran da Alhaji Bello Ibrahim a matsayin SSA kan sabuwar kafar yada labarai.

Sauran sun hada da Alhaji Umar Sani Mataimaki na musamman kan tsare-tsare, Alhaji Kabiru Yusuf, Direkta Janar kan harkokin tsare-tsare da Alhaji Saidu Maishanu mai'aikacin FRCN Pride FM a matsayin Babban Manajan Hukumar Kula da Gidan Rediyo da Talabijin na Zamfara (ZRTV).

Sanarwar ta aka fitar a yammacin ranar Juma'a ta ce dukkan wadanda aka yiwa nadin za su kama aiki nan ta ke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel