Kannywood: Za mu dauki mataki kan masu shirya fina-finan soyaya - MOPPAN

Kannywood: Za mu dauki mataki kan masu shirya fina-finan soyaya - MOPPAN

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa, MOPPAN, Kabiru Maikaba ya ce nan ba da dade wa ba kungiya za ta kafa dokar hana masu shirya fina-finai yin fim din soyaya.

A hirar da Maikaba ya yi da BBC a ranar Alhamis, ya koka kan yadda masu shirya fina-finai na Kannywood suka mayar da hankali a kan fim din soyaya a maimakon isar da wasu sakonni da za su iya kawo canji a al'umma.

"Kimanin kashi 80 cikin 100 na fina-finan da mu keyi a Kannywood na soyaya ne amma ba haka ya dace ba. Mene ya sa muka mayar da hankali a kan fim din soyaya duk da cewa mun san akwai wasu abubuwan daban da za mu iya yin fim a kai?

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

"Yankin arewa yana cike da dimbin tarihi. Mene ke hana masu shirya fim din mu su rika yin fina-finai da za su nuna tarihi da al'adun mu? Muna gaba da yin zabe kuma bayan zaben za mu saka dokokin da za su hana yin fim din zallar soyaya.

"Za mu hukunta duk wani mai shirya fim ta hanyar dakatar da shi na lokaci mai tsawo kuma zamu cigaba da yin hakan har sai mun kawo gyara a masana'antar na fim."

Wasu masu shirya fina-finai da su kayi hira da majiyar Legit.ng sunyi tsokaci kan matakin da MOPPAN ke shirin dauka.

Wasu na ganin dokar za ta kawo koma baya a masana'antar yayin da wasu kuma suna ganin hakan shine abinda ya dace ayi.

Hassan Dalhat, wani mai tallata fina-finan Kannywood ya ce matakin zai kawo gyara a Kannywood amma wasu da dama za su rasa ayyukansu idan ba suyi takatsantsan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel