Buhari ya yi sallar Juma'a a Saudiyya (Hotuna)
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sallar Juma'a a babban masallacin Makkah da ke Saudiyya tare da kimanin shugabanin kasashen duniya 53 da daruruwan mabiya addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa Buhari da sauran shugabanin kasahen duniya sun tafi kasa mai tsarkin ne domin hallartar taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) karo na 14.
Taron wadda Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ne mai masaukin baki zai fara ne misalin karfe 12 na dare.
Wadanda suka yiwa shugaba Buhari rakiya sun hada da gwamnonin jihar Osun, Niger da JIgawa.
An sa ran shugaba Buhari zai gana da wasu shugabani kasashen duniya kafin ya dawo gida Najeriya a ranar Lahadi kamar yadda NAN ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana
Asali: Legit.ng