Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye

Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye

- Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye

- An dai ga Teema Makamashi tana habaici a shafinta na Instagram inda

- Duka 'yan matan sun yiwa Sanatan waka da fasta ta siyasa sun kai masa, inda ya dauki hoto da kowaccen su

Wani rikici da ya barke tsakanin matan Kannywood guda biyu Teema Makamashi da Fati Mohammed, inda suke rikici akan Sanatan jihar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye.

Rikicin ya samo asali ne lokacin da Teema Makamashi take gargadin Fati Mohammed akan kwaikwayenta da tayi wurin yiwa Sanatan waka.

Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye

Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye
Source: Facebook

Ga abinda Teema Makamashi ta rubuta a shafinta na Instagram:

"Keda samun soyayyarsa sai dai ki gani daga nesa"

Tauraruwar Teema Makamashi wacce ita ce ta fara yiwa Sanata Dino Melaye waka, tayi wannan habaicin ne ga Fati Mohammed wacce ta kwafeta.

Teema tayi rubutun ne a shafinta na Instagram inda ta cigaba da cewa, "Ga wani sabon salon shima idan zaki yi, banda waka, tunda kome nayi sai kinyi, kina tare da bakar wahala indai ni zaki dinga kwaikwaya."

KU KARANTA: Wata kwamiti a jihar Bauchi ta kaiwa gwamnan jihar wani tsari data binciko da zai taimaka wurin samar da ayyukan a jihar

Tauraruwar ta saka hoton fastar siyasa da tayi wa Sanatan a shafinta na Instagram a lokacin da tayi wadancan habaicin.

An ga Fati Mohammed ta yiwa Sanata Dino Melaye waka da kumaa fasta ta siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel