Ba sandar girma Ganduje ya mikawa sabbabbin Sarakuna ba – Kwankwaso

Ba sandar girma Ganduje ya mikawa sabbabbin Sarakuna ba – Kwankwaso

Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi tir da raba masarautun Jihar da gwamna Abdullahi Ganduje yayi kwanaki.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa rashin sanin darajar manyan gari ne ya sa gwamnatin jihar Kano ta yanzu ta kirkiro wasu sababbin masarauta a Kano.

Rabiu Kwankwaso ya bayyana wannan ne a lokacin da yayi wata diguwar hira a gidajen rediyon jihar Kano a gidansa. An yi wannan hira da ‘yan jarida ne a jiya Laraba 29 ga Want Mayun 2019.

Injiniya Kwankwaso yayi ikirarin cewa kudi aka biya ‘yan majalisar dokoki domin su sauke Sarki Muhammadu Sanusi II daga kan karagar mulki. Kwankwaso yace N500, 000 aka ba ‘yan majalisar.

KU KARANTA: Abba Yusuf yayi kaca-kaca da Ganduje bayan ya barka fadar Kano

Ba sandar girma Ganduje ya mikawa sabbabbin Sarakuna ba – Kwankwaso

Kwankwaso yace sababbin Sarakunan Kano kokara suke rikewa
Source: Facebook

A cewar Sanatan mai shirin barin-gado, wannan abu da gwamnatin Ganduje tayi, ya lalata jihar Kano, kuma zai yi wa kowa illa nan gaba domin ana bukatar manyan Sarakuna masu daraja a kasa.

Babban ‘dan siyasar ya kuma yi magana a kan zaben 2019 da aka yi a jihar Kano inda yace an zubar da mutuncin al’ummar jihar, kuma Duniya ta san cewa Abba Yusuf ne ya lashe zaben da aka yi bana.

Bayan nan kuma ‘dan majalisar ya tofa albarkacin bakinsa a game da zaben shugaban kasa inda yace APC ta gaza ba shugaba Buhari kuri’u miliyan 5 din da aka yi masa alkawari a Kano kafin zaben 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel