Najeriya tafi kowacce kasa yaki da rashawa a duniya – Inji Ribadu

Najeriya tafi kowacce kasa yaki da rashawa a duniya – Inji Ribadu

Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa dayi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa duk duniya babu kasar dake yaki da rashawa kamar Najeriya, kamar yadda ya shaida ma jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu yayin da yake tattaunawa a bayan fagge a bikin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu daya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Farawa da iyawa: Wani sabon gwamna yace ba zai iya biyan albashin N30,000 ba

Ribasu ya shaida ma majiyarmu cewa idan aka kwatanta da adadin mutanen da aka kama aka kuma gurfanar dasu gaban kotu da kuma yawan makudan kudaden da aka kwato, hakan zai tabbatar da cewa babu kasar dake yaki da rashawa kamar yadda Najeriya take yi.

“Babu wanda zai yin irin wannan namijin kokari kamar shugaba Muhammadu Buhari, yana kokari matuka, kuma ya kamata mu bashi goyon baya, ya kamata mu taimaka masa wajen ganin ya kammala aikin nan.

“Idan har muka gaza wajen yaki da rashawa, akwai yiwuwar komai zai tabarbare, don haka dole ne mu tashi tsaye mu yaki cin hanci da rashawa, kuma dolene mu kawo karshensa.” Inji shi.

Malam Nuhu Ribadu ne mutum na farko daya fara rike mukamin shugaban hukumar EFCC bayan kafuwarta a shekarar 2004, daga bisani kuma tsohon shugaban kasa Yar’adu ya cireshi daga mukamin a shekarar 2007.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel