Tambuwal ya nemi afuwar mutanen Sokoto

Tambuwal ya nemi afuwar mutanen Sokoto

A ranar Talata ne gwamnan jihar Sokoto, Aminu Wazairi Tambuwal, ya rushe majalisar zartarwa ta jiha tare da sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar.

Tambuwal ya shaida wa masu rike da mukaman siyasar da ya sauke cewar yana yi musu fatan alheri a aiyuka da harkokin da zasu shiga a nan gaba tare da yi musu godiya bisa gudunmawar da suka bashi.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwa na karshe da ya yi da masu rike da mukaman siyasa a ranar Talata.

A watan Yuli na shekarar 2018 ne Tambuwal ya sauke dukkan masu rike da mukaman siyasar da ya fara nada wa bayan ya canja sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Ya ce bai fuskanci wani tarnaki da zai hana shi barci ba a mulkinsa saboda ya gudanar da gwamnati ne bisa gaskiya da adalci.

Tambuwal ya nemi afuwar mutanen Sokoto
Tambuwal
Asali: UGC

"Ina yin barci cikin kwanciyar hankali saboda na gudanar da gwamnati bisa gaskiya, zan iya kare dukkan wani mataki da na dauka.

"A matsayina na dan adam, mai yiwuwa ne na taba saba muku, a saboda haka ina neman afuwar ku.

"Amadadin majalisar zartar wa, ina neman afuwar dukkan jama'ar jihar Sokoto a kan dukkan wata shawara ko wani mataki da muka dauka wanda baku ji dadinsu ba," a cewar Tambuwal.

DUBA WANNAN: Sanatoci sun nuna kyashi a kan N160m da FIRS ta ware domin walwalar direbobi 850

Masu rike da mukaman siyasar da gwamnan ya sauke sun hada da kwamishinoni, masu bashi shawara da masu taimaka masa na musamman.

Wasu daga cikin wadanda aka sauke da suka hada da sakataren gwamnati, Bashir Garba, shugaban ma'aikata, Buhari Bello, kwamishinan kudi, Suleiman Usman da kwamishiniyar ilimi, Aisha Madawaki, sun yiwa Tambuwal godiya bisa damar da ya basu ta hidimtawa jama'a da jihar Sokoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel