An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe

An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe

- 'Yan sanda sun samu nasarar ceto rayuwar mata da 'ya'yan dan majalisar nan da akayi garkuwa da su a jihar Gombe

- Sun yi nasarar ne bayan sun samu hadin gwiwar 'yan kungiyar sa kai na yankin wurin gumurzu da 'yan bindigar

Rundunar 'yan sandan jihar Gombe tare da hadin gwiwar 'yan kungiyar sa kai, sun yi nasarar ceto rayuwar matar dan majalisar wakilan nan mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye, Yaya Bauchi Tongo da 'ya'yansa guda biyu, daga hannun masu garkuwa da mutane.

A cewar wani mutumi da ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa wasu mutane da ba a san suwaye ba sun kai hari kauyen Tongo dake karamar hukumar Funakaye, dauke da manyan bindigu a cikin daren ranar Litinin da misalin karfe 8 na dare, a lokacin da mutane ke yin sallar 'Tarawih', inda suka yi awon gaba da matar dan majalisar da 'ya'yansa guda biyu.

An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe

An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe
Source: Twitter

Mutumin ya bayyana cewa an ceto rayuwarsu ne a dajin Kurugu, bayan an yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigar da misalin karfe 4 na daren yau Talatar nan.

Mun samu rahoton cewa jami'an tsaron sun samu taimakon 'yan kungiyar sa kai na yankin, hakan yasa suka samu nasara a kan 'yan bindigar, inda suka ajiye iyalan dan majalisar, da babur guda biyu suka ranta cikin daji.

KU KARANTA: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa guda 10 na shekarar 2019

Rahotanni sun nuna cewa matar dan majalisar ta samu rauni a bayanta sanadiyyar harsashi da ya taba ta, amma yanzu haka tana karbar magani a babban asibiti na Bajoga.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, SP Obed Mary Malum, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel