Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa guda 10 na shekarar 2019

Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa guda 10 na shekarar 2019

- Majiyarmu Legit.ng ta yi kokarin zakulo muku fitattun 'yan wasan kwallon kafa guda goma na kakar wasa na wannan shekarar

- Lionel Messi, Cristiano Ronaldo da Mohammad Salah sune manyan 'yan wasan da suka fito a na farko a jerin 'yan wasan

Jiya Litinin ne 27 ga watan Mayu mujallar ESPN ta wallafa sunayen 'yan wasan kwallon kafa guda goma da suka fi kowa a duniya, mujallar ta wallafa sunayen 'yan wasan da kuma sunayen kungiyoyi da suke buga kwallo a shafinta na yanar gizo.

Mujallar ta ce, "Mun kammala hada manyan 'yan wasa na 2018 - 2019 baya da watanni tara da suka gabata, sai dai an samu wasu sabbin fuskoki a cikin manyan 'yan wasan guda goma na wannan karon, sannan kuma wasu da yawa sun fita daga cikin jerin 'yan wasan a wannan karon.

Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa guda 10 na shekarar 2019

Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa guda 10 na shekarar 2019
Source: Facebook

"Kamar yadda kalanda ta nuna, yanzu haka mun gama tattara sunayen manyan 'yan wasan kwallon kafa na kakar wasa na bana," in ji mujallar ESPN kamar yadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

KU KARANTA: Tirkashi: Donald Trump ya ce 'yan Afirka ba mutane ba ne

Ga sunayen kamar yadda mujallar ESPN ta wallafa a shafinta na yanar gizo:

1. Lionel Messi Barcelona

2. Cristiano Ronaldo Juventus

3. Mohammad Salah Liverpool

4. Kylian Mbappe Paris Saint German (PSG)

5. Sergio Aguero Manchester City

6. Karim Benzema Real Madrid

7. Timo Werner RB Leipzig

8. Raheem Sterling Manchester City

9. Eden Hazard Chelsea

10. Edinson Cavani Paris Saint German (PSG)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel