Murnar cika shekaru 54: Babban burina na shiga aljanna – Inji Ministan Buhari

Murnar cika shekaru 54: Babban burina na shiga aljanna – Inji Ministan Buhari

Ministan sufuri, kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Chibuike Rotimi Amaechi ya bayyana bayyana farin cikinsa na cika shekaru hamsin da hudu, 54, a rayuwa, inda yace a yanzu babban burinsa shine ya shiga aljanna bayan mutuwarsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu yayin da yake jawabin godiya ga Allah a cocin St Gabriel Chaplaincy dake unguwar Durumi na babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Kowa ya debo da zafi: Matashin da yayi wanka a cikin kwata saboda Buhari yayi nadama

Murnar cika shekaru 54: Babban burina na shiga aljanna – Inji Ministan Buhari
Amaechi da matarsa
Asali: UGC

Da yake jawabi, Amaechi yace a yanzu ya gode ma Allah tunda ya samu nasara a siyasar Najeriya, sa’annan kuma ya cika shekaru 54 cikin koshin lafiya, don haka yake mika godiya ga Allah saboda wannan baiwa da Yayi masa.

Amaechi ya bayyana cewa yayi fama a lokacin dayake yaro, sakamakon mahafinsa mai karamin karfi ne, don haka yayi addu’a tare da fatan samun Najeriya mai kyawu ta yadda yan Najeriya ba zasu sha wahala sosai ba wajen samun biyan bukata.

Haka zalika Ministan yayi alkawarin taimaka ma talakawan dake zuwa cocin ta hanyar bayar da kyautan buhun shinkafa guda goma goma a kowanne wata ga cocin domin ta rarraba musu.

Ita ma uwargidar ministan, Judith, ta gode ma Allah da yayi ma mijinta tsawon rai, sa’annan ta bayyana jin dadinta da yadda yake kokari wajen farfado da sufurin jirgin kasa a Najeriya, inda tace tana fatan zai cigaba da aiki tukuru idan ya sake samun dama a gwamnatin Buhari.

A ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 1965 aka haifi Amaechi a kauyen Ubima cikin karamar hukumar Ikwerre ta jahar Ribas, sunan mahaifinsa Fidelis Amaechi, mahaifiyarsa kuma Mary Amaechi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel