Kowa ya debo da zafi: Matashin da yayi wanka a cikin kwata saboda Buhari yayi nadama

Kowa ya debo da zafi: Matashin da yayi wanka a cikin kwata saboda Buhari yayi nadama

Masu iya magana suna cewa “Kowa ya debo da zafi, bakinsa” wani matashi dan asalin jahar Bauchi mai suna Muhammad Aliyu Sani, wanda aka fi sani da Ali Gayu wanda ya yi wanka a cikin kwata tare da shan ruwan kwatan duk don murnar tazarcen Buhari yace yayi nadama a yanzu.

Ali Gayu ya bayyana haka ne a cikin wata hira da yayi da jaridar Leadership Hausa, inda yace duk da irin hadarin daya jefa kansa ta hanyar kwankwadar ruwan kwatami don nuna farin cikinsa da nasarar da Buhari ya samu a zaben 2019, amma babu wani abin alherin da gwamnatin tayi masa.

KU KARANTA: Rikicin siyasar Zamfara: Kanin Sheikh Ahmed Gumi ya zama dan majalisar tarraya a PDP

Kowa ya debo da zafi: Matashin da yayi wanka a cikin kwata saboda Buhari yayi nadama
Kowa ya debo da zafi: Matashin da yayi wanka a cikin kwata saboda Buhari yayi nadama
Asali: Facebook

A cewar Ali mai shekaru 23 “Na sha suka da zagi na sha yabo a lokacin dana sha ruwan kwata tare da yin birgima a cikin kwatan duk don tsabar soyayya ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk da cewa kwata najasace amma Allah Ya kareni babu abinda ya sameni.

“Amma abin mamaki kuma abin damuwa shine har yanzu wannan gwamnatin da nayi abinda nayi don ita kamar bata san na yi ba, babu wanda ya damu da lafiyata a cikinsu, wanda idan da ace na samu wani abin alheri daga wannan lamari na tabbata da wasu sun karu dani.” Kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.

Aliyu ya tabbatar da cewa shifa har yanzu bai ga ribar wannan sadaukarwa da yayi da rayuwarsa ba, don yayi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari data kula da masoyanta, wadanda suka yi mata hidima.

“A yanzu babban burina shine gwamnati ta gayyaceni zuwa taron rantsar da shugaban kasa, kuma na gana da shugaban kasa gaba da gaba, don hakan ya zame min abin alfahari, idan kuma ba haka ba, tabbas ta tabbata gwamnatin Buhari bata damu da masoyanta ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel