Hukumar 'yan sanda ta cafke 'yan ta'adda 43 a jihar Bauchi

Hukumar 'yan sanda ta cafke 'yan ta'adda 43 a jihar Bauchi

Bayan makonni uku da nadin sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Bauchi, CP Habu Sani, hukumar 'yan sanda a jihar ta samun nasarar cika hannu da ya miyagun 'yan ta'adda 43 da suka afka tarkon ta.

Hukumar 'yan sanda ta cafke 'yan ta'adda 43 a jihar Bauchi
Hukumar 'yan sanda ta cafke 'yan ta'adda 43 a jihar Bauchi
Asali: Facebook

Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar yayin gabatar da jawaban sa a ranar Asabar da ta gabata, ya ce sabon salo na tsari da kuma kudirin inganta harkokin tsaro a jihar ya yi tasiri wajen cafke miyagun masu ta'ada da suka hadar da masu garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran ababe na sharri.

CP Habu Sani ya bayanin cewa cikin 'yan ta'adda arba'in da uku da suka shiga hannu tuni kotu ta zartar da hukuncin kan guda takwas yayin da ragowar talatin biyar ke ci gaba da kirdadon hukuncin da zai rataya a wuyan su.

A yayin da hukumar 'yan sandan jihar Bauchi ta sake zani wajen daura damarar tunkarar kalubale na rashin tsaro, ta cafke miyagu 26 masu ta'addancin fashi da makami da kuma 'yan sara suka gami da fataucin miyagun kwayoyi.

KARANTA KUMA: Ma'aikata sun yiwa Gwamna Yari bankwana a jihar Zamfara

Sabon kwamishinan 'yan sandan yayi bajakolin kayayyakin ta'ada da miyagun ke ribata wajen zartar da ta'addanci a jihar Bauchi da suka hadar da makamai na nau'ikan bindigu daban-daban, muggan kwayoyi, maganin tari na Kodin da kuma yankunan takardun kudi na Dalolin Amurka.

Mai garin birnin Bauchi Nuhu Jumba, cikin jawaban sa ya yaba da sabbin tsare-tsaren sabon kwamishinan 'yan sandan jihar biyo bayan nasarorin da hukumar tsaro ke ci gaba da samu cikin tsawon makonni uku da suka shude.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel