Gwamna Masari ya soke bikin ranar 29 ga watan Mayu

Gwamna Masari ya soke bikin ranar 29 ga watan Mayu

Gwamnatin jihar Katsina ta soke dukkanin abubuwa domin bikin ranar 29 ga watan Mayu sai dai rantsar da gwamna da mataimakinsa kawai za a yi domin yin alhinin mutuwar wadanda yan bindiga suka kashe wannan makon a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, a jiya Alhamis, 23 ga watan Mayu yace an yanke hukuncin ne bayan wani mumunan hare-hare da yan bindiga suka kai a wasu yankunan jihar.

“Hakan kuma domin taya iyalai da sauran mutanen da suka rasa masoyansu ko dukiyarsu sakamakon mumunan harin yan bindiga alhini ne,” inji shi.

Gwamna Masari ya soke bikin ranar 29 ga watan Mayu

Gwamna Masari ya soke bikin ranar 29 ga watan Mayu
Source: UGC

A cewarsa hare-haren ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama sannan ya jikkata da dama yayinda wasu suka zama marasa galihu.

“Don haka, an soke wasu tsare-tsare da akan shirya domin bikin illa kawai wanda ya zama dole wato rantsar da gwamna da mataimakinsa kamar yadda yake a sashi 185(1) na kundin tsarin 1999,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Daukan dala ba gammo: An kama mutane 140 da suka shirya yi ma Buharu juyin mulki

Yayinda yake rokon mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu, Inuwa ya bukace su da su jajirce wajen addu’o’i, mussamman a wadannan ranakun karshe na Ramadana, don zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel