An sake rufe wani gidan shakatawa a jihar Kano saboda ayyukan masha'a

An sake rufe wani gidan shakatawa a jihar Kano saboda ayyukan masha'a

Hukumar Kula da Yawon Bude Ido na Jihar Kano ta sake rufe wani wurin shakatawa, Piccolo Lounge da ke kan Tukur Road a Nasarawa GRA a birin Kano.

A hirar da ya yi da manema labarai bayan rufe wurin a ranar Laraba, shugaban hukumar, Abdullahi Gwarzo ya ce sun rufe wuraren shakatawa biyu a cikin watanni uku da suka shude a jihar.

Ya ce hukumar ta rufe wurin ne sakamakon korafe-korafe da mazauna unguwar su kayi kan 'ayyukan masha'a' da ake aikatawa a wurin.

An sake rufe wani gidan shakatawa a jihar Kano saboda ayyukan masha'a

An sake rufe wani gidan shakatawa a jihar Kano saboda ayyukan masha'a
Source: UGC

DUBA WANNAN: An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

A cewarsa, hukumar ta gudanar da bincike a kan korafe-korafen inda ya gano cewar wurin shakatawar ba ta samu lasisi ba daga hukumar ba kana an bude wurin ne a rukunnin gidajen jama'a.

Mr Gwarzo ya ce ya yi basaja yayin da ya ziyarci wurin domin gudanar da bincike.

"A yayin gudanar da binciken mu bayan mun samu korafi daga mazauna unguwar, na ziyarci wurin amma ba su gane bincike na zo yi ba. Na zauna a wurin har misalin karfe 1 na dare inda nayi ta ganin abin takaici. Na ga 'yan mata da samarin su suna ta shan shisha.

"Akwai samari da 'yan mata da yawa suna ninkaya kusan tsirara. Hakan yasa dole mu rufe wurin har sai an gyara dukkan kurakuren da ake yi," inji shi.

Wasu daga cikin mazauna unguwar sun yabawa hukumar bisa matakin da ta dauka na rufe wurin shakatawar inda suka ce wurin ya zama musu fitina a unguwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel